2023: SHURE SHURE BAYA HANA MUTUWA. TA TABBATA DUK MARASA KISHIN NIGERIA, KWANKWASO SUKE TSARO

  



Karyar da yan jamiyyar APC Gandujiyya suke yadawa na cewa akwai rigima a cikin kwankwasiyya ta jihar kano tare da ikirarin cewa akwai yi'uwar yan kwankwasiyyar su sauya jamiyya nan kusa, ya nuna kururu cewa Jamiyyar APC Gandujiyya ta gamsu dacewa lokacin tashin alkiyamar ta ya riga da yazo. 


A yau ne muka tashi da wani labari mai ban al'ajabi na kararrayi da qazafi ga jamiyyar PDP kwankwasiyya ta jihar kano wanda cikin kankanin lokaci asiri ya tonu na mutanen da suka bada kwangilar yada propagandar. 


Wannan yana kara tabbatar da nasarar tafiyar kwankwasiyya ba'a iya jihar kano ba amma har kasar Nigeria baki daya idan akayi la'akari da sakonnin da suke cikin takardar. Maganar da aka rawaito a cikin takardar na bayanin rikici a cikin tafiyar kwankwasiyya,  wannan ya kara tabbatar wa da al'umma irin bita da kulle tare da daukko kwangiloli kalala na rusa Arewa da wasu mutane marasa daraja ake zarginsu da shi musamman a bangaren gandujiyya. 


Domin kuwa, a Bangaren Kwankwasiyya har izuwa yanzu babu wani abu da yake nuna cewa akwai rabuwar kai , mussamman idan akayi la'akari da yadda kullum tafiyar take kara bunqasa a fadin kasa. Haka zalika ita kwankwasiyya kamar yadda kowa yasan tsarinta, yasan cewa akwai jagoranci mai inganci wanda duk wani mabiya yayi amanna dashi. 


Dan haka duk ireren propaganda irin wannan da wasu daga cikin jamiyyar APC ta kasa da kuma APC Gandujiyya  suka maida hankali sukeyi akan tsarin kwankwasiyyar , al'ummar kasa suke watsi dashi cikin gaggawa. 


Na tabbata mai karatu zai yadda dani, idan nace tun da aka kafa gwamnatin Jamiyyar APC a kasa , idan akayi la'akari za'a ga cewa babu tsarin da jamiyyar APC  take adawa dashi kamar tafiyar Kwankwasiyya, duk da cewa ba Jamiyya bace. 


Wannan ba wani abu bane yasa illa irin tsoro, kiyayya, kyashi da wasu makiya Nigeria suka hade kai sukeyiwa Jagoran Tafiyar Kwankwasiyyar wato  Sanata Dr Rabi'u Musa kwankwaso , duba da irin karbuwa da yayi a wajen al'umma wanda a yanzu haka duk fadin Arewa babu wanda yake da masoya yan dangwale kamar shi. 


Haka zalika ta fannin Gwamnati, Suna adawa da kwankwason ne domin shi babu gwamnati a hannunshi amma yayiwa al'umma abubuwan alkhairi bila adadin wanda gwamnati ta kasa yi mussamman ta fannin gina matasa da basu ilimi. 


Kar ka data kar ka rage wannan shine makasudin abunda yasa suke tsoron ya samu dama , domin idan ya kasance shine shugaban kasa, toh shakka babu zai shafe duk wani abun alkhairi da wani dan siyasa yataba yi a Nigeria domin kuwa shi yana sa capacity kuma ya gwada a jihar Kano angani.  


Wannan ce tasa al'umma suke kaunarshi kuma suka jajirce akanshi, haka zalika sukuma makiyanshi suka gamsu da cewa idan basu fito da hanyar saka rudani ba a cikin zukatan jama'a to shakka babu ko a jamiyya Mai Hoton Zakara Kwankwaso ya tsaya takara to shakka babu al'umma shi zasuyi. 


Post a Comment

0 Comments