Siyasa: PDP tayi martani na musamman ga Abdullahi Abbas

 



Jam'iyyar PDP a jihar Kano, karkashin shugabancin Hon. Shehu Sagagi, tayi martani kan kalaman shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, wanda yace dole sai sun kwace zabe kuma ba abinda zai faru, abinda suka aikata a mazabar Gama ta karamar hukumar Nasarawa a zaben 2019, shi zasu kuma aikatawa a zaben 2023, sannan suci kutumar uban yan Kwankwasiyya.


PDP tayi martanin ne yayin wata ziyara da wasu magoya bayan Kwankwasiyya suka kawo mata, inda shugaban jam'iyyar, Shehu Sagagi, yace su da Allah suka dogara, amma zasu bi koyarwa ta Annabin rahama, Annabi Muhammad (SAW), ba'a cizon mumini sau biyu a rami daya, kuma ko cikin suratul Al-Imran, aya ta 173, Allah ya fadi yadda munafukai suka sanar da musulmai cewa ga kafurai can sunyi runduna domin gamawa da musulmai (A yakin uhud), amma sai maganar ma ta kara musu imani, suka ce Hasbunallahu Wani'imal Wakeel, inji Sagagi.


Bugu da kari, Sagagi yace wannan magana da shugaban APC yayi, ba zata tsorata magoya bayansu ba, kuma har yanzu cigaba suke samu ba ci baya ba, dasu da dan takararsu na gwamna, Abba Kabir Yusuf, kana yayi kira ga shugabannin siyasa, dasu dinga tsaftace harshensu wajen furta magana, domin dorewar zaman lafiya a tsakanin al'umma, amma dai su daga garesu ba zasu biyewa irin wancan barin zance na marasa daraja ba, kamar yadda ya bayyana.


A karshe, shugaban na PDP, yayi kira ga jami'an tsaro da ma'aikatan shari'a, dasu kaucewa shiga sha'anin siyasa, su tsaya wajen yiwa kowa adalci, tabbatar da gaskiya akan mai gaskiya da kuma tabbatar da rashin gaskiya akan mara gaskiya.



Post a Comment

0 Comments