Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta zargi jam`iyyar APC mai mulki da gazawa wajen kyautata rayuwar al`ummar kasar.
PDP ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa cika alkawuran da ya yi lokacin neman zabe, don haka ya kamata sauya salo ko ya yi murabus.
Amma jam`iyyar APC ta yi watsi da wannan zargin, tana cewa PDP ce musabbabin tabarbarewar tsaro da sauran al`amura a Najeriya, don haka ba ta bakin sukar gwamnati.
Jam`iyyar PDP ta yi zargin cewa jam`iyyar APC ta rabe ne da halin da Najeriya ta samu kanta ta fuskar tsaro shekara ta 2015, har ta yi wa `yan Najeriya kumfar-baki da alwashin magance matsalar, alhali babu wani shirin da ta yi.
Hasali ma a cewar PDP, duk alkawuran da shugaba Buhari ya yi a baka ne kawai, kuma an kai magaryar tukewa a Najeriya, don haka ya kamata ta gusa gefe ya ba da wuri ga masu yi da gaske.
Senata Umar Ibrahim Tsauri shi ne sakataren jam`iyyar PDP na kasa, ya shaida wa BBC cewa "sun yi alkawarin cewa za su kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, za su gyara tattalin arzikin kasar, za su yi yaki da cin hanci da rashawa. Idan an duba yanzu za a ga cewa duk abuuwan da aka fada babu daya wanda aka samu ci gaba a cikinsa sai dai ci baya."
"Yau dan Najeirya ba ta me zai yi yake ba, a'a, ta yadda zai kwana lafiya yake yi. Don haka ko dai shugaban kasa ya kafa dokar ta-baci kan tsaro, ko ya kira taron tsaro na kasa: dukkan wani wanda ya taba zama jami'in tsaro ya zo ya bayar da gudunmawarsa, idan haka ta faskara ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda", in ji Sanata Tsauri.
Jam`iyyar PDP dai ta ce a shirye take ta hada-kai da jam`iyya mai mulki don sama wa Najeriya mafita, tana nuna takaicin cewa, APC ba ta yi amfani da irin shawarwarin da PDP ta yi ta bayarwa a baya ba.
Sai dai jam`iyyar APC a nata bangaren ta yi fatali da zargin da PDP ke yi, tana cewa da ba a san asali kuli ba da sai ya ce day alkama aka yi shi.
APC ta zargi PDP da tabka kura-kuran da suka jefa Najeriya a halin da ta samu kanta na tsananin talauci, wanda a bangare guda ya ta`azzara matsalar tsaro.
Wannan ne ma ya sa APC ke cewa PDP ba ta da bakin magana.
0 Comments