"dayeke Jawabi a taron masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar PDP a Kano, Sanatan yayi Jan hankali tare da zaburar da Jagororin Kwankwasiyya, da duk wani wanda yai imani da tafiyar Kwankwasiyya, koda ya waiwaya kan Yan Majalisar dokoki na Jihar kano Yan Kwankwasiyya, yaja hankalinsu da cewa aikin Danmajalisa ya kasu kashi uku (3)
Ka kai Kudiri ga al'umar da kake wakilta, da kuma samar da burtsatse da tallafin kudi da kayan abinci da sauransu, duk abune me muhimmanci, "Amma mafi muhimmanci a wajanmu shine kafito kayi rigima da gwamna akan abin dayake zai cutar da al'uma!!, kamar ciyo bashin dazai cutar da Jama'ar Kano yagadawa mutane Talauci har zuwa jikokinmu, matukar kayi haka to babu tantama kasamu (automatic ticket) ma'ana zaka koma kujerarka babu hamayya.
Amma koda kayi burtsatse ka raba kayan abinci da mashina, matukar zaka kewaye kakarbi filaye ka rantaba hanu don aci gaba da cutar da al'umar Jihar Kano, a gadamusu bashi, to kasani idan Allah yasa muna raye a 2023 baka da tabbas sai mun duba wanda ya cancanta.
Sanatan yayi wannan jawabine a lokacin daya ziyarci Kano a lokacin bikin Karamar Sallah.
Allah ya taimaki Kwankwaso da Kwankwasiyya .
0 Comments