Fada da cikawa: Kwankwasiyya ta sake kafa tarihi a fannin ilimi.





Gidauniyar Kwankwasiyya, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta sanar da fara cike neman gurbin tallafin karatun digiri ga dalibai biyu maza biyu mata daga kowacce jiha, wato mutum hudu kenan daga kowacce jiha cikin jihohi 36 dake Nigeria, da zata dauki nauyin karatunsu a jami'ar Mewer dake Abuja, a kalla mutane 148 kenan baki daya a jimilla.


Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, gidauniyar ta kwankwasiyya ta bada dama ga duk mai bukata ya ziyarci shafin yanar gizo na makarantar www.miu.edu.ng. domin yin rijistar neman wannan tallafi, ko kuma ya tuntube su akan mail na kdfscholarship@miu.edu.ng ko kuma lambar waya 09015269767, domin karin bayani, kamar yadda yake cikin sanarwar da shugaban daliban da suka rabauta da tallafin karatu karkashin kwankwasiyya, Dr. Yusuf Kofar Mata, ya fitar ta hannun Ibrahim Adam.


Wannan dai shine karon farko da wata gidauniya a Nigeria zata dauki nauyin karatun dalibai a dukkan jihohin kasar zuwa makarantar jami'a mai zaman kanta, wacce tazo daga kasar India ta sanadin shi madugun kwankwasiyyar, domin ya kai musu dalibai masu karatun digiri na biyu a shekarar 2019, jim kadan bayan sun fadi zabe, abinda wasu mutane suke mamaki, amma sai yace shi ba saida mulki zai taimaki al'ummarsa ba, wanda har takai ga siyar da wasu kadarorinsa domin wancan aiki.


A yanzu dai dama ce ga kowa, ba sai wanda yake da ra'ayin siyasar Kwankwasiyya ba, za'a dauki mutane hudu daga kowacce jiha cikin jihohi 36 na Nigeria harda Abuja, bisa cancanta ba alfarma ba, kamar yadda gidauniyar ta sanar, harma ta bukaci mutane da su cire tunanin suna da sanayya da wani jigo a Kwankwasiyya, domin hakan bazaiyi tasiri ba matukar dai basu cancanta ba, cancanta ita ke bada dama a Kwankwasiyya, tun ana gwamnati har yanzu da ake wajen gwamnati, a cewarsu.

Post a Comment

1 Comments

  1. TSOKACHI
    Salam alaikum lallai wannan abin ayabane bisa wannan namijin kokari, ammafa za'ai tuyane amanta da albasa domin dunbin mabiya ko magoya bayan wannan tafiya ta kwankwasiyya DALIBAINE ahalin yanzu Su wanne tanadi ake masu?

    ReplyDelete