Dan Kwankwasiyya Ya Dauki Nauyin Yara 50, Domin Yin Karatu Kyauta,Tun Daga Primary, Har Zuwa Secondary.

 



Daya Daga Cikin Daliban Da Mai Girma Sen Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Tura Karatu Kasar Wajan,Shima Ya Dauki Nauyin Wasu Yara 50, Domin Yin Karatu Kyauta,A Kar Kashin Gidauniyarsa Mai Suna (Namama Charity Foundation)  Alhaji Abdullahi Namama  Yana Daya Daga Cikin Daliban Da, Mai Girma Jagora Sen Dr Rabiu Musa Kwankwaso,Ya Dauki Nauyin Karatunsa Kyauta,A Lokacin Yana Gwmanan Jahar Kano Daga 2011 Zuwa 2015.


Alhaji Abdullahi Namama An Tura Shi Karatu Ne, A Daya Daga Cikin Makarantu Mafi Tsada A Duniya, Mai Suna International University Of East Africa(IUEA) Kampala A Kasar (Uganda) A 2014, Kuma Dan Asalin Karamar Hukumar Kumbotso Ne, A Cikin Bayanansa Namama Ya Bayyana Jin Dadinsa,Sanda Aka Dauki Nauyin Karatunsa Zuwa Kasar Wajan Domin Yin Karatu Kyauta, Inda Shima Yayi Alkawarin Daukar Nauyi Wasu Dalibai Domin Yin Karatu Kyauta Idan Har Ya Sami Damar Haka, Kuma Gashi Cikin Ikon Allah, Allah Mai Iko Ya Cika Masa Wannan Buri Nasa Na Alkairi,Kuma Daga Kar Kashin Namama Yace Akwai Wani Shiri Da Yake Yi Nan Gaba Kadan, Domin Taimakawa Al'umma Musamman Yan Asalin Karamar Hukumar Kumbotso,Dama Jahar Kano,Domin Suma Su Sami Ilimi Kyauta.


An Daukin Nauyin Karatun Wadanda Nan Daliban Ne,A Makarantar Madarasatul Ahlu Badar,Littahfizil Qur'ani Dake Sheka Gidan Gabas, Dake Karamar Hukumar Kumbotso.


Duk Mai Bibiyar Alhaji Abdullahi Namama, Yasan Ba Wannan Ne Karo Na Farko,Daya Kaddamar Da Taimamawa Al'umma Ba,Idan Ba'a Mantaba Haka Yayi Sanda Ana Cikin Yanayi Na Corona Virus,Ya Taimakawa Al'umma Dai Dai Gwargwado.


Muna Adu'a Allah Ya Cigaba Da Sawa Dukiya Albarka, Allah Kuma Ya Kara Daukaka, Allah Ya Karo Mana Irin Wadanda Bayin Allah Masu Son Cigaban Al'umma,A Duk Inda Suke Ameen Summa Ameen.


Post a Comment

0 Comments