ILLAR DA GWAMNATIN GANDUJE TA YIWA KANO, (001). Nazari akan Dajin SAMBISA na Jami'ar North-West Kano.

 






Wannan jami’a, tana daya daga cikin makarantun gaba sakandare guda ashirin da shida(26) da gwamnatin Engr. Dr rabiu Musa Kwankwaso ta kirkiro a zangon mulkinsa na biyu a jihar kano daga 2011 zuwa 2015, da nufin habbaka cigaban ilimi a jihar Kano, Arewa da kasa baki daya.

Idan zaku iya tunawa Jihar Kano na daya daga cikin jihohin dake da koma baya a fannin ilimi sakamakon yawan al’umma da take dasu da kuma karancin guraben karatu a jami’o’in dake fadin Najeriya. Amma daga zuwan kwankwasiyya tayi namijin kokari wajen habbaka ilimi a jihar kano, ta kirkiro wannan jami’a domin fadada damar samun gurabe ga yan asalin jihar kano, Arewa da kasa baki daya.


Abin dubawa anan shine,  gwamnatin Kwankwaso ta kirkiri wannan Jami’a  tayi manyan gine gine a cikin wannan makaranta wasu ta gama wasu bata gama ba, amma abin tambaya anan shine, ko me yasa Gwamnatin maici ta Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi watsi da karasa wadannan gine-gine da kuma yin watsi da aikace aikace na gudanarwa a wannan jami’ar?


"Wannan daliline   yasa Daliban wannan makaranta suke kiranta da SAMBISA Wato (Permanent Site)"


Wata majiyarmu ma tace hatta motoci da sauran kayan aiki na wannan makarantar  sun lalace an gaza gyrasu da kuma samar da wasu, duk da ikirarin da gwamnatin ganduje take na dorawa akan aiyyukan gwamnatocin da suka gabata.


A binciken da kwankwasiyya reporters tayi ta gano cewa,  gwamna Ganduje yasa wannan jami'ar ne a siyasa  musamman  a rikicin siyasar sa da mai Gidansa Kwankwaso,  Kwankwasiyya Reporters ta zanta da wasu mutanen Jihar Kano inda kaso casa'in 90/%  daga cikinsu, sun bayyana siyasa ce ta haifar da wannan matsalar. Haka zalika mafi akasarin ayyukan da kwankwaso ya faro gwamnatin sa, Ganduje ya yi watsi da su, saboda wannan rigima.


A karshe muna kira ga Yankasuwa, Malaman addini, Shuwagabannin al'umma, Kungiyoyi da sauran al'ummar jihar Kano da su bawa  gwamna Ganduje Shawara akan ya cire siyasa a fannin  Ilimi, saboda Siyasa daban harkar Ilimi daban, haka kuma muna kira ga gwamna da ya waiwayi wannan makaranta da sauran Makarantu da yayi watsi da su, domin cigaban Ilimi a jihar Kano.


Har Yau 18/03/2021 Gwamnatin Kano bata Kammala gine-ginen Gwamnatin Kwankwaso ba a Makarantar kuma ita bata  kara koda gini kwaya  daya ba, in banda gine ginen TETFUND wanda Dr Baffa Bichi l ya Kawo lokacin yan shugaban Hukumar TETFUND.


Post a Comment

0 Comments