Engr. Rabiu Musa Kwankwaso A Mahanga Ta Adalci.
Tabbas Dukkan Wanda Ya Sanni Ya San Bani Da Wata Alaqa Ta Kusa Ko Ta Nesa Da Tsohon Governor, Tsohon Senator Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso FNSE. Amma Tabbas Adalci Wani Mizani ne Da Masu Hankali Ke Auna Al-Amarin Rayuwa Dashi.
Tabbas Salon Yanayin Da Sen. Engr Rabiu Musa Kwankwaso yake Gudanar Da Wasu Abubuwan na Alheri da Gina Mutum Ta Fuskar Ilimi fa Dogaro da Kai.
A Tarihin Siyasar Kano Tun Bayan Tsohon Governor Marigayi Alhaji Abubakar Rimi, Kano Bata sake Samun Wani Governor Wanda Yayiwa Harkar Ilimi hidima Lokacin Yana Cikin Gobnati ba da kuma Bayan Barinsa Gobnyi ba Kamar Engr. kwankwaso.
ya Gina Makarantun Jami'a (University Guda Biyu)
College kuwa Yanzu Haka Bani Da Masaniyar iyakarsu.
Haka Institute Ya Gina Babu Adadi a Fadin Cikin Birnin Kano Da Kauyukan Kano.
daga cikinsu Zanyi Sampling.
1) Nursing And Midwifery (Madobi)
2) Nursing and midwifery (Danbatta)
3) School of Health (Bebeji)
4) School For Remedial Studies (Tudun Wada)
5) Fishery (Bagauda)
6) Sport institute (Kura)
7) Informatics (Kura)
Engr. kwankwaso Ya Dauki Nauyin Matasa Domin kammala Karatun PhD Dama Da 250, MSc da MA. Sama da 1500, Ya Dauki Nauyin Karatun Matasa A Matakin First Degree daga Matasa Adadin Da Zaiyi Wahala Wani Ya Bayar Da Yawansu, A Ciki da wajan Nigeria.
Tabbas Dukkan Wanda Yake Da Kishin Jahar Kano Da Al-Ummar Jahar Kano At least ya Kamata Yayiwa Kwankwaso Abubuwa kamar Haka:-
1) Allah Ya Karbi Wannan Aiyukan NASA na Alheri.
2) Allah Ya Yafe Masa Abin da Aikata Na Kuskure.
3) Allah Ya Taimaka Masa Wajan Cimma Bukatunsa Na Taimakawa Al-Ummarsa.
4) Allah Abubuwan da Yake Nema Na Siyasa, Allah Ka Saukake Masa Hanyar Samunsu.
5) Allah Ka Hadashi Da Mutanen Kirki, Wadanda Zasu Cigaba Da Karfafarsa Wajan Taimakawa Al-Ummarsa.
6) Abu Na Karshe Allah Ya Kyautata Bayansa, Ya Sanya Shi Cikin Ni'amrsa, ya Faranta masa kamar Yanda ya Faranta Ran Dubbun Talakawa.
Daga Karshe Har yanzu Ni Ina Tare Da Tafiyar Siyasar Sen. Malam Dr. Ibrahim Shekarau CON. Sardaunan Kano Da Kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR.
Lawan Adam Yahya Yakasai.
16/03/2021
1 Comments
I wish him all the very best
ReplyDelete