Sanin kowa ne yanzu a yan siyasar da ka'iya neman kujerar shugaban kasa kaf dinsu babu wanda yake samun fatan alkhairi daga al'umma daban daban na fadin Nigeria Sama da Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, mussamman idan akayi la'akari da yadda matasa maza da mata suke rububin binshi duba da yadda ya juri akidar gina yan'uwansu matasa ta fannin basu ilimi tare da tsaya musu wajen ganin sun ginu sun zama mutanen kansu sun taimakawa yan'uwansu da abokan arziki.
Idan muka dubi lissafin jefa kuri'a a lokacin zabe, mai karatu zai yadda dani idan nace babu rukunin al'umma dake jefa kuri'a da ya kai matasa da kuma iyaye mata. Izuwa yanzu ba abu bane boyayye, kowanne dan Nigeria mussamman yan siyasa masu lissafi , kowa ya riga da yasan indai magana ake ta cin zabe da kuri'ar yan kasa babu wanda zai iya ja da Sanata Rabiu Musa kwankwaso.
Masu lissafin cin zabe da yawan kuri'a sukan daura lissafinsu akan abubuwa kamar haka:, karbuwar Jamiyyar da yankin da dantakara ya fito, karbuwar dan takara a jihar shi da kuma gogewa a harkar tafi da mulki da iya jagoranci na siyasa. A wasu lokutan wasu masu lissafin sukan iya auna zurfin aljihun dantakara wacce a yanzu duba da yanayi da aka tsinci kai a karkashin Jamiyya mai mulki zai yi wuya al'umma su sayar yancin su na son ganin gabansu tayi kyau, dan kuwa idan har suka sake suka kara yadda sukayi "dana sani" da fadin cewa gwanda gwabnatin baya da wacce suka zaba toh babu shakka zasu tsunduma cikin wani yanayi wanda babu wanda ya isa ya iya harsashen shi a yanzu.
Idan mai karatu ya dauki ma'aunen sannan ya hada da sauran nashi, zaiga cewa a yanzu a duk wayanda ake tunanin zasu iya fitowa zawarcin wannan kujerar babu wanda zai iya karawa da Sanata kwankwaso zummar yasamu tikitin takara.
Na farko, izuwa yanzu Kwankwaso dan jamiyyar PDP ne hasalima shine ubanta shine uwarta a jihar Kano jihar da tafi kowacce jiha yawan kuri'a ta al'umma da ta delegates. A yau idan kwankwaso yana takara na tabbata babu wani dan takara da yake Kasar Nigeria zai iya samun kaso 20% cikin 100% na kuri'ar alummar Jihar Kano kama daga zaben fidda gwani har izuwa zaben du gari.
Na biyu, maganar karbuwa wajen al'umma, ba sai na bata lokaci ba, sanin kowane yanayi irin na karbuwar da kwankwaso ya samu yanzu a fadin Nigeria mussamman yankin arewa duba da yadda ya daukin tsarin hassasa harkar ilimi a matsayin tsarin da zai iya kawowa kasa ci gaba ta hanyar bawa matasa ilimi domin fito da sabbin dabaru da zasu kai kasar Nigeria tundun muntsira tare da rage zaman banza wanda shine ummul haba'isi wajen tabarbarewa tsaro da ake fama dashi yanzu.
Na uku shine iya jagoranci, wanda yana daya daga cikin ginshikai da yazama wajibi ace duk mai neman irin wannan kujera yana dashi. Idan muka dauki musali akan hadaddiyar Kungiyar kwankwasiyya wacce Engr Kwankwaso yake jagoranta, ba abu bane boyayye, kaf Nigeria zaka tarar babu wani dan siyasa da yake raye da ya taba gina irin wannan kungiya tare da samar mata da tsaruka masu nagarta wa'enda nan da shekaru masu yawa al'umma zasu ci gaba da kasance akansu. Kowa yasan irin hazikai da masu ilimi da suke cikin wannan katafariyar qungiya wacce ta ginu akan akidu masu inganci mussamman ta fannin gina matasa, koyar da iya shugabanci ga matasa tare da samar da democradiyya mai inganci da sauransu a fadin Nigeria. Qungiyar kwankwasiyya a yanzu tashiga kowanne lungu da sako na kasar Nigeria, dalilin haka a wash lukatan Jamiyya mai mulki take wa qungiyar Kallon Babbar abokiyar hamayya ta fannin siyasa.
Zanso na ci gaba da zayyano ire iren wayannan maunen dake nuna yadda alkaluman siyasa suke haska Kwankwaso fiye da kowanne dan takara da alumma suke yiwa sha'awar zama shugaban kasa a shekarar 2023 wanda yake tafe nan da yan shekaru da basu gaza biyu ba ga mai yawan rai. Duba da yawan hujjoji da ma'aune da nake dasu, zan so na dakata anan naci gaba a wani karon, nayi kira ga al'ummar kasa , a kullum su dunga duba yanayin da suke a baya , sannan su duba yanayi da suke ciki a yanzu suyiwa kansu gata wajen tabbatar da sun kasance cikin yanayi mai inganci a gabansu. Haka zalika jami'yyun siyasa wayanda suke da alhakin fiddawa al'umma dan takara, ya zama wajibi su ajiye son zuciyarsu su kalli abun da kan iya zamewa al'umma alkhairi dasu baki daya. Sannan zanso al'umma masu son asamu saunyin mulki nagari da suyiwa hujjoni kyakkyawar fahimta su hada da nasu, zasu ga cewa yanzu dama ce tazo, dan na tabbata duk da bana duba, amma da zummar ance yau Rabi'u Kwankwaso ne yake takara mussamman a jamiyyar PDP, toh ba makawa da yardar Allah da karfin ikonshi za'a samu sauyin mulki a Nigeria.
Daga karshe ina fatan Allah ubangiji yayi mana jagora ya zabamana da wayanda mukeyiwa fatan alkhairi da Nigeria baki daya abun da zai fiye zame mana alkhairi. Amin
0 Comments