Da alama dai tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara shirin mamaye siyasar 2023 mai zuwa tun daga yanzu, cikin wani salo da ake iya ganin kamar dai gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya tsaya kallon ruwa ne, kuma kwado zai masa kafa, domin an hango tsohon shugaban hukumar tattara haraji na jihar Kano, Sani Abdulkadir Dambo, sanye da jar hula, tare da Kwankwaso a garin Abuja.
Sani Abdulkadir Dambo, guda ne cikin manyan ginshikan siyasar Ganduje, a garinsu na Dawakin Tofa, wanda Ganduje da kansa ya nadashi mukamin shugaban hukumar tattara haraji na jihar Kano, kafin daga baya ya ajiye aikinsa bisa radin kansa a wata ranar Alhamis 9th ga watan Afrilu 2020, dukda cewa daga baya gwamnatin Kano tace bata karbi takardar ajiye aikin nasa ba, daga baya kuma ta rubuta masa takardar kora da kafa kwamitin bincike kan zargin yin badakala.
Tun a lokacin dai, Kano Online News, ta rawaito cewa, Dambo ya cika bakin cewa a shirye yake kuma yana bawa gwamnatin Kano shawara, akan ta kaishi kara Kotu, abinda kuma har kawo yanzu da Dambon ya sauya sheka zuwa Kwankwasiyya, gwamnati bata shigar dashi karar ba kamar yadda ya bukata, hakan tasa wasu ke ganin cewa Dambo yana da gaskiya akan tirka-tirkar, yayin da wasu ke ganin kawai dai kawaici da dattako gwamna Ganduje ya nuna, domin dabi'a ce tasu ta fulani.
0 Comments