Yanzu Hatta Mafi Akasarin Yan Siyasarmu Sunfi Maida Hankali Wajen Ganin 'Ya'yansu Sunyi Karatu, Yayin Da Suke Halin Ko In Kula Da Karatun 'Ya'yan Talakawa, Da Zummar Nan Gaba 'Ya'yansu Ne Kawai Zasuyi Mulki Bamu Ba, Kuma Hakan Zata Iya Kasancewa Matukar Bamuyi Karatu Ba, A Matsayinmu Na 'Ya'yan Talakawa, Saboda Bakar Aniyar Wasu, Tsarin Inganta Ilimi Na Badashi A Kyauta Ma Saida Suka Soke, Ga Tsadar Rayuwa Da Suka Kakabawa Al'umma, Shi Yasa Yanzu Kullum Karatu Yake Ja Baya.
Ilimi Hasken Rayuwar Dan Adam, Masana Sun Tabbatar Da Cewa Al'umma Tana Samun Cigaba, Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Ne Kawai Idan Akwai Ilimi. Ta La'akari Da Wannan jagoran Talakawa Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Yayi Hubbasa Wajen Tabbatar Da Cigaban Ilimi Tun Daga Tushe, Wajen Gina Makarantun Firamare Da Sikandire, Duk Nigeria Shine Ya Bullo Da Tsarin Ciyar Da Daliban Firamare Abinci A Makaranta, Wanda Yanzu Wasu Gwamnoni Harma Gwamnatin Tarayya Suka Kwaikwaya, Sannan Yana Bada Littattafai Kyauta Da Kayan Makaranta Don Inganta Ilimi, Uwa Uba, Ilimin Kyauta Ake Yinsa A Gwamnatinsa, Tun Daga Firamare Har Zuwa Manyan Makarantun Gaba Da Sikandire.
Shine Gwamna Daya Tilo, Da Ya Gina Jami'oi Har Guda Biyu, Wato Jami'ar Kimiyya Da Fasaha Dake Wudil, Wacce Yayi A Zangon Mulkinsa Na Farko, Da Kuma Juma'ar Northwest A Zango Na Biyu, Ganin Cewa Jami'a Daya Tak Garemu A Jihar Kano, Wato Bayero University Kano, Kuma Ta Gwamnatin Tarayya Ce, Ga Kuma Yawan Al'umma Dake Kano, Guraben Karatu Suna Wuya Garemu. Sannan Yayi Gine Gine A Manyan Kwalejojin Gaba Da Sikandire A Jihar Kano.
Bai Tsaya Haka Nan Ba, Ya Gina Wasu Cibiyoyin Ilimin Gaba Da Sikandire Don Koyon Ilimin Sana'oi Guda 26, Wanda Mafi Yawa A Yankunan Karkara Akayi Su, Domin Saukaka Musu Samun Ilimin Gaba Da Sikandire Cikin Sauki, Sannan Akwai Wadanda Basa Samun Sakamakon Credit 5 Zuwa Sama Da Zasu Shiga Jami'a Dashi Ba, Kuma Suna Da Basirar Da Ya Kamata Su Shiga, Wadannan Institutes Zasu Taimaka Musu Wajen Samun Fandisho Na Shiga Jami'a.
Yayi Tsarin Bada Tallafin Karatu Kyauta, Ga Dubban Dalibai Yan Asalin Jihar Kano, Zuwa Jami'oin Cikin Gida Nigeria Da Kasashen Ketare, Wanda Dukkansu 'Ya'yan Talakawa Wadanda Aka Kaisu Bisa Cancanta Ba Alfarma Ba, Sukayi Karatun Digirin Farko, Na Biyu Harma Na Uku A Fannonin Ilimi Daban Daban, Wanda Yanzu Mafi Yawansu Suka Aiki Da Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kamfanoni Da Sauransu, Sun Zama Ababen Alfahari Ga Al'umma.
Al'ummar Nigeria Musamman Matasa, Mu Yunkura Wajen Ganin Mun Rabauta Da Wanda Yake Burin Ganinmu Cikin Rayuwa Managarciya, Kwankwaso Shine Yafi Dacewa A Wannan Yanayi Da Muka Samu Kai, Mu Hadu Waje Guda Domin Samunsa, Yin Hakan Shine Taimakon Kanmu, Yan Uwanmu, Abokanmu Da Sauran Al'umma.
0 Comments