Bamu san wani Mahmina ba, mu Sagagi muka sani a Kano - PDP




Uwar jam'iyyar PDP ta kasa, ta kara jaddada batunta na cewa basu yarda da shugabancin kowa a jihar Kano na jam'iyyar PDP ba, sai Shehu Wada Sagagi, wato tsagin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda aka zaba a matsayin shugabanni jam'iyyar PDP na jihar Kano babu dadewa, kuma zasu jagoranci jam'iyyar tsawon shekaru hudu.


Bayanin hakan ya fito ne daga sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Umar Ibrahim Tsauri, wanda yace sun amince da shugabancin Sagagi, haka itama hukumar zabe ta kasa INEC ta yarda, kuma ba zasu saurari kowa ba a shugabancin nasu na Kano sai Sagagi. 


Kamar yadda aka sani, akwai shugabancin jam'iyyar PDP a Kano, bisa shugabanta Mahmina Bako Lamido, na tsagin Ambasada Aminu Bashir Wali, wanda a kwanakin baya ma, mun kawo muku yadda kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, yace da shugabancin Sagagi suka aminta, babu wani bangare a jam'iyyar tasu a Kano.



Post a Comment

0 Comments