TARIHIN MARIGAYI ALH. MUSA SALE KWANKWASO (1927-2020)

 


"Anhaifi Marigayi Alh. Musa Sale Kwankwaso a unguwar Daburau dake garin Kwankwaso, a yankin karamar hukumar Madobi dake birnin Kanon Dabo, a shekarar 1927"; kamar yanda Muhammad Adamu Kwankwaso ya wallafa. Yafara neman ilimin addinin musulunci a matakin farko ashekarun yarinta, inda yakaranci al-Qur'ani mai girma. Daganan ya karanci ilimin zamani a (Elementary School) wanda yabashi damar kwarewa afannin rubutu da karatu. Ya karanci litattafan addini da dama tundaga shekarun yarinta, samartaka, har sanda girma ya cimmasa.


Annada Marigayi Alh. Musa Sale Kwankwaso matsayin Maigarin Kwankwaso a shekarun samartaka a 1954, lokacin yana dan shekara (27) a duniya. Yarike wannan matsayi na Maigarin Kwankwaso tsawon shekaru (46), daga 1954 zuwa 2000.


A shekara ta 2000, mai Martaba Marigayi Alh. Ado Bayero yanada Marigayi Alh. Musa Sale Kwankwaso sarautar Majidadin Kano tareda daga matsayinsa daga mai garin Kwankwaso zuwa Hakimin Madobi. Yarike sarautar Hakimin Madobi tsahon shekaru (19), daga 2000 zuwa 2019. Bayan kirkirar sabbin masarautu da gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje tayi a shekarar 2019, Alh. Musa Sale Kwankwaso yasami sabon matsayi na MAI NADA SARKI a masarautar Karaye (Karaye kingmaker). A watan Janairu na shekarar 2020, annada Alhaji Musa Sale Kwankwaso Sarautar Makaman Karaye, sarautarda akai bikinta awatan daya gabata watan Nuwamba na shekarar da muke bankwana da ita.


Alh. Musa Sale Kwankwaso yasami nasarar gudanarda mulki a karkashin sarakunan Kano guda (4):

1-Mai Martaba Marigayi Murabus Sarki Sanusi na farko.

2-Mai Martaba Marigayi Sarki Muhammad Inuwa.

3-Mai Martaba Marigayi Alh. Ado Bayero

4-Mai Martaba Murabus Sarki Muhammad Sunusi na 2. 


Allah yakarbi rayuwar Mai martaba Makaman Karaye Alh. Musa Sale Kwankwaso adaren Juma'a a ranar 25/12/2020. Ya rasu yabar mata 2 araye, Yaya (19) tare da jikoki da dama. Cikin manya-manyan yayansa maza akwai:

1-Tsohon Gwamnan jihar Kano, tsohon ministan tsaron Nigeria, tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, tsohon dan takarar shugaban kasa Eng. Rabiu Musa Kwankwaso (Jagoran dariqar Kwankwasiyya na duniya).

2-Alh. Garba Musa Sale (mai garin Kwankwaso).

3-Inuwa Musa.

4-Alh. Yahaya Musa (Dogon Sarki).

5-Umar Musa

6-Lawan Musa

7-Gambo Musa

8-Maimuna Musa

9-Safiyya Musa

10-Bilkisu Musa

Da dai sauransu.


Allah yajikansa da gafara. Allah yakarbi shahadarsa. Allah yakyauta makwancinsa. Allah yasa Annabi (S.A.W) yakarbi bakuncinsa. Allah yahaskaka kabarinsa. Allah yahada kan zuri'arsa ya albarkacesu. Allah yabawa yaya, yan uwa, jikoki da abokan arziki hakurin jure wannan babban rashi, ameen.


Translated:

Aminu Saidu (Meenan Kwankwasiyya)

Chairman Kwankwasiyya Promoters Kano State. From the Department of History and International Studies Northwest University Kano.

Referee:

Muhammad Adamu Kwankwaso

From Department of Education Bayero University Kano.

Post a Comment

0 Comments