Labari: Kwankwasiyya ta musanta batun komawa jam'iyyar APC

 



An samu yaduwar jita-jita tsakanin al'ummar Nigeria a wannan dan tsakanin, musamman a shafukan sada zumunta na zamani, kan cewa tsohon gwamnan jihar Kano, jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai fice daga jam'iyyarsa ta PDP wacce aka kafata dashi tun a shekarar 1998, zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, abinda ya janyo cece-kuce da sharhi daga mutane mabambanta, musamman yadda ake ganin shugaban kwamitin rikon jam'iyyar APC na kasa, gwamnan jihar Yobe Maimala Buni, ya himmatu wajen zawarcin jiga-jigan PDP ciki harda gwamnoni, abinda ya sanya shakku a zukatan wasu mutane, dukda dai a yanzu a iya cewa babu kanshin gaskiya a waccan jita-jita. 


Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya yiwa jam'iyyar PDP takarar mataimakin Gwamna a Kano yayin zaben 2019, shine mai magana da yawun Kwankwasiyya na kasa, yace wannan zance ne mara tushe balle makama, abu ne wanda bada wurinsu ya fito ba, ya fito ne daga yan jam'iyyar APC, suke yadawa don yanzu sun gano amfani da tasirin jagoran nasu, sai kuma yan korensu da suke amfani da sunan su yan jam'iyyar PDP ne suna yiwa APC aiki, irinsu Ambasada Aminu Wali, amma babu abinda zasu yiwa Allah sai godiya, domin ko yanzu an kara nuna nagarta, jajircewa da daukakar Kwankwaso, har jam'iyya mai mulki tana fatan ya dawo cikinta, suna ganin siyasarsu bata cika sai ya dawo cikinsu.


Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da shafin Kwankwasiyya Reporters ya wallafa a jiya juma'a, inda yace ai Kwankwaso jagoran Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne, kuma shugabansa ne, bazai yiwu Kwankwaso ya dawo karkashinsa ba, tunda dai tsarin jam'iyyar APC ne duk gwamna shine jagora a jiha, kuma ma Kwankwaso ya rasa inda zai koma jam'iyya sai a kafar yada labarai ta yanar gizo? Kawai dai APC sun rasa mutanen da zasuyi tutiya dasu ne, shima Buharin da sukayi tutiya dashi, yanzu ya bayyana kunnen Jaki ne da baya bawa Kura tsoro, shi yasa suka hango Kwankwaso, a cewarsa.


Gwarzo ya kara da cewa, ai dama APC ta kware a yada propaganda, ko a bara ma sunce tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan zai koma cikinsu, gwamnan Rivers Nyesom Wike ma sunce zai koma cikinsu, yanzu har shugaban PDP na kasa Uche Secondus ma sunce APC zai koma, kaga kenan basu da wani kwakwkwaran dan siyasa mai nagarta, sai kallon gidan PDP, domin duk wata rigar da ta isa magana ta siyasa a yanzu tana cikin PDP, kuma ba'a siyasa da rigar aro, idan baku da yan siyasa baza ku iya ba, inji kwamared. 


Bugu da kari, kwamared din ya musanta batun cewa akwai alaka mai karfi ta siyasa tsakanin Kwankwaso da gwamnan Zamfara Bello Matawalle, ko gwamnan Bauchi Bala Muhammad, ganin cewa ana jita-jitar Matawalle ya koma APC kafin Kwankwaso ya biyo bayansa, yace basu da wata alaka sai ta jam'iyya, domin Kwankwaso indai kana cikin jam'iyyar da yake, kuma baka kokarin tada fitina, to yana tare dakai, baya bakin cikin wani dan jam'iyya ya karu da basirar da Allah ya bashi, amma dukkansu ba yaran Kwankwaso bane, bashi ya tsayar dasu takara ba, ba mai gidansu bane, amma yau ace kwamared ne zai koma APC to babu laifi idan ance Kwankwaso yana da masaniya, kuma hatta gwamnonin APC suna matukar ganin girman Kwankwaso ba iya na PDP ba, saboda haka girmamawa ce tsakaninsu amma ba maigidansu bane, don ko a zaben shugabancin jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yamma da ya gagara yiwuwa a kwanakin baya, gwamna Matawalle bai marawa Kwankwaso baya ba, Tambuwal ya marawa baya.


A karshe kwamared Aminu Abdussalam, yaja hankalin mutane da a daina masabta fitar gwamna Matawalle ko wani ma da Sanata Kwankwaso, ya kuma kara yin kira da ayi watsi da batun cewa Kwankwaso zai koma APC, wai harda alkawarin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa, da ministoci guda biyu, da rushe shugabancin APC a Kano a bashi, inda yace ai dama shugaban APC a rushe yake a halin yanzu, kwamiti ne suke rikon jam'iyyar, kuma tunda har an bashi mataimakin shugaban kasa, ya kamata masu yada karyar su bayyana wannene kuma shugaban kasar, domin sai an samu shugaba sannan ake samun mataimaki, to amma zantuttukan suna kara nuna daraja da nagarta da Kwankwaso. 



Post a Comment

0 Comments