Yau naga ikon Allah, yan Gandujiyya suna da rashin ta ido, wato a rayuwa idan mutum ya kasance jinka wanda daukarsa sai an taro, abin burgewa ne, yau an wayi gari mabiya gwamnatin jihar Kano karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, suna bukatar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kawo dauki ga daliban sikandire da suka fadi jarabawar Qualifying, ya taimaka ya biya musu kudin rijistar rubuta jarabawar NECO, sai abin ya bani mamaki don banyi tsammani ba.
Daukin wadannan daliban bai wuce na gwamnati ba, saboda bata son ta biyawa yara dalibai kudin NECO shi yasa bata sakamakon jarabawar Qualifying da wuri ba sai a satin da hukumar NECO zata rufe rijistar jarabawarta, ai ku yanzu gwamnati kuka kwancewa kanku zani a kasuwa, kuna da gwamnatin jiha, sanatoci uku, yan majalisar tarayya 24, yan majalisar dokoki guda 28, ciyamomi guda 44, Kansiloli 484, Amma duk kuke neman taimakon wani single person da bashi da mukamin Koda Kansila, kaga kunsan zai iya abinda ya gagare ku, dukda ikirarinku na cewa kunyi masa ritaya daga siyasa, yau kuma a matsayinku na masu ludayi akan dawo, kune da rokon dan ritaya, dukda cewa bakwa bashi fansho.
Yanzu fa Kwankwaso ba magana ake ta jihar Kano ba, yanzu Jagora bana yan Kano bane ne kadai, magana ake ta Nigeria, yanzu haka an fara cike gurbin tallafin karatu dazai dauki nauyin mutane hudu daga kowacce jiha a Nigeria, zuwa jami'ar Mewer ta kasar India a reshenta dake Abuja, ina fatan kuma yan Gandujiyya zaku nema, don Kwankwaso mutum ne da baya jin nauyin daukar nauyi. Masu siyasar karamar hukuma, sune da wannan aikin, shi Kwankwaso saidai yayi a matsayin abinda gwamnati ta kasa, kuma kunsani, kuma wannan ba komai bane a taskar gudummawarsa wa al'umma, mu Kwankwasiyya ilimi ne ginshiki, a gwamnatinsa shi yake biyan kudin NECO, ga duk dalibin da yasa Credit 5 a jarabawar Qualifying, koda kuwa babu darasin turanci da lissafi, harda kyautar rijistar JAMB ga wadanda suka duba da farko.
Ku ai saidai ku bawa wasu labari, akwai daliban Kano dake karatu a Sudan, suka dinga rokon Ganduje akan ya biya musu kudin makaranta, don hukumar makaranta ta koresu sai sun biya kudi, ga babu abinci, Ganduje cewa yayi idan suka kara magana to saidai kowa ubansa ya biya masa, ai kuwa nan take ubansa ya kama hanyar sai gashi kasar Sudan, to balle kuma kudin jarabawar Qualifying, gaskiya nayi mamaki, amma kuma naji dadi da mabiyan gwamnatin Ganduje suka yarda da gazawarta da kansu, suka aminta da kokarinmu akan al'umma.
Alhamdulillah, Allah ya ƙarawa Kwankwaso lafiya da nisan kwana mai albarka, ya bashi babban rabo don al'ummar jihar Kano, da Nigeria baki daya su amfana.
0 Comments