Sen. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso yace "Duk wani mai son cigaban Kano dan Kwankwasiyya ne, ba sai yasa jar hula ba. Ya kara da cewa duk wani mai neman nakansa dan Kwankwasiyya ne".
Saboda duk wani mai son Cigaban Kano yasan wacce gudunmawa Dr Kwankwaso yabayar a fannoni daban, musamman bangaren ilimi.
Mai kishin Kano da mai neman nakansa babu san zuciya a tare dasu.
Idan kana so ka auna cigaban ko wacce al,umma sai ka fara duba wacce kullawa suka bawa ilimi da Matasa, domin shine haske rayuwa, gishirin rayuwa da shi ake gina tunani makyau.
Dukkan al'ummar da tayiwa ilimi rukon sakainar kashi, sai tazamo kamar ba,a taba yinta a doron duniya ba.
Magana ake akan ilimi a jahar Kano a yau.
Makarantun gaba da sakadire guda ashirin da daya (21) da Gwamnatin Dr Kwankwaso ta kirkira wanda wannan Gwamnati ta Gandujiya ta rufe.
Daga lokacin da aka rufe wadannan Makarantu anyi kiyasi, Jahar Kano tayi asara babba, wanda da yanzu jahar Kano ta yaye akalla dalibai sama da dubu sabi'in (70 000)
Ya jama,ar Jahar Kano wannan Kauna ce ?
0 Comments