Wani bincike da jaridar Legit.ng tayi, ta bayyana cewa ta gano a yanzu babu wani dan siyasa mai tasiri musamman ta fuskar magoya baya kamar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma yana cikin jerin tsofaffin gwamnoni guda shida a Nigeria, wadanda suke da karfin fada aji a yankinsu, dukda cewa basa kan kujerar mulki ta gwamna.
Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, Kwankwaso yayi mulkin jihar Kano a matsayin gwamna a shekarar 1999 zuwa 2003, sannan ya kara zama gwamna a karo na biyu daga shekarar 2011 zuwa 2015, amma dukda haka al'umma suna rububinsa, ba a jihar Kano kawai ba, harma da sassa daban daban na kasa Nigeria.
Ragowar tsofaffin gwamnonin sun hada da, tsohon gwamnan jihar Lagos, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido CON, tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Delta, Cheif James Onanefe Ibori, sai kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.
"Ana danganta yanayin siyasarsa da ta Malam Aminu Kano. A duk inda ya shiga, ruwan jajayen huluna ake gani. Babu shakka halayyarsa ta gina kananan 'yan siyasa da tallafawa jama'a ne yasa yake da wadannan mabiyan."
0 Comments