Jam'iyyar PDP nayiwa al'ummar Karamar hukumar Gwarzo Barka da Shan ruwa.
Jam'iyyar PDP nakira ga al'ummar Karamar hukumar Gwarzo da su cigaba da yin koyi da darasusan da suka koya cikin azumin watan Ramadan, tare da yin addu'o'i akan halin da Kasar nan take ciki.
Haka kuma jam'iyyar na jajantawa al'ummar Karamar Gwarzo bisa yadda mulkin jam'iyyar APC ya mai dasu koma baya, Karamar hukumar Gwarzo ta samu koma baya, babu ayyukan cigaba kamar yadda aka saba samu a gwamnatoci baya.
Jam'iyyar na takaicin yadda wannan gwamnati ta jam'iyya APC takasa tabuka komai a Karamar hukumar, duk da yawan masu rike da madafun iko da suke acikin wannan gwamnati, kuma 'yan Asali karamar hukumar ne, wannan abun kunya ne.
Kasan cewar yanzu a wannan gwamnatin Karamar hukumar ta rabauta da mukamai da dama Wanda ya hada da Kwamishina guda biyu, MD guda uku, da sauran manya mukamai, Amma duk suntashi a banza babu katabus da suke domin cigaban wannan karamar hukuma.
Duba da gazawa da Jam'iyyar APC tayi a wannan karamar hukuma, Jam'iyyar PDP ke kira ga Al'ummar wannan yanki da su dawo rakiyar wannan jam'iyya, su rungumi jam'iyyar PDP itace zata fito dasu daga halin kunci da jam'iyyar APC ta saka su. Saboda haka Jam'iyyar PDP ta tabayi kungani.
Allah ya albarkaci wannnan Karamar hukuma tamu mai albarka. Allah ya kawo mana damuna mai albarka. Allah yasa ayi Sallah da kuma bukukuwan Sallah lafiya, Allah yasa anyi Ibada karbabu. Amin
0 Comments