Ramadan: Kwankwasiyya ta bukaci daukin addu'oi daga musulmai

 



Tafiyar siyasar Kwankwasiyya a jihar Kano ta bukaci daukin addu'oi daga al'ummar musulmai cikin wannan kwanaki goman karshe na watan azumin Ramadan, bisa wasu bukatu nata na samun zaman lafiya da adalci, da kuma batun sace matashin nan dan Kwankwasiyya mai suna Abubakar Idris (Abu Hanifa Dadiyata), dan asalin jihar Kano, mazaunin Kaduna, mai mace daya da 'ya'ya biyu mata, wanda aka sace kusan Shekaru biyu da suka gabata.


Shugaban kungiyar Kwankwaso Dawo-Dawo 2011, kuma dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Gwale, Hon. Yusuf Babangida Sulaiman (Dawo-Dawo), shine ya bukaci a taya su da addu'oin a wannan goman karshe na watan Ramadan, domin rokon Allah ya bayyana shi cikin yanayi mai kyau, kamar yadda dan majalisar ya bayyana a shafinsa na tuwita. 


Dan majalisar yayi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a Nigeria, dasu kara himma wajen ganin cewa sun kubutar da Dadiyata daga hannun wadanda suka sace shi, domin hakki ne akansu na su tabbatar da cewa sun kare rayuka da dukiyoyin al'umma. 



Post a Comment

0 Comments