Ta yiwu da yawan ku kun ci karo da manyan ƴan siyasar Ƙasar nan daban-daban, sai dai na san ba lallai bane ya kasance kun taɓa tsayawa ku nazarci halayya da ɗabi'un su ba, ballantana har ku iya riskar matakin da za ku fahimci, shin mutane ne masu daraja ko kuwa?
Cewar mutum mai daraja ba wai yana nufin mutumin da yake da ƙarfin iko na kuɗi ko kuma mulki bane. Ba kuma yana nufin girman rawanin malunta bane, ka na baya ɗaukar ma'anar girman rawani irin na sarauta.
Daraja tana ga mutumin da yake tsayuwa akan gaskiya da kuma tabbatar da gaskiya ko da kowa zai gujeka. Daraja ba a iya furucin baki take tsayuwa ba, tana tafe ne da zahirin al'amuran mutum na yau da kullum waƴanda su suke ɗauke da ma'anonin halaye da kuma ɗabi'un sa.
Kana iya zamantowa mai mulki irin na siyasa ko kuma na sarauta, amma ba lallai bane ya kasance kana cikin rukunan mutane masu daraja ba matuƙar ba amfanarka talakawanka suka yi ba.. Haka kuɗi ko kuma tarin dukiya ba za su sanya al'umma su kalleka a matsayin mai daraja ba har sai sun shaida alfanun dukiyar taka ga ci gaban rayuwarsu.
Kwankwaso mutum ne mai magana ɗaya da bai san munafunci ko yaudara ba. Barazana ko kwarjini basa hana shi ya furta zai yi ko ba zai yi ba. Kai tsaye yake bayar da amsa akan dukkan ƙudirin da yazo gaban shi ba tare da yaji nauyin ka ba. Hatta maƙiyansa sun shaide shi kan cewa ba mayaudari bane, sannan kuma ba maƙaryaci bane. A siyasance, ban taɓa jin ya furta zai yi abin da yasan ba zai aikata ba. Kuma bai taɓa bayar da aikin al'umma ba tare da ya bibiya ba. A karan kansa ya yarda da cewa shi shugaba ne, dan haka komai a wuyansa ya rataya.
Shi ne ɗan siyasa na farko a tarihin siyasar Ƙasar nan da har gobe kusan kaso 95 na al'ummar Ƙasar nan basu taɓa ganin matarsa ba, sai dai ko a hoto. Hoton ma kuma sai dai in a sace ya fito, kuma shi ɗin ma ba zai haura biyu zuwa uku ba. Babu wani muƙamin siyasa da ya rage da bai yi ba fa ce shugabancin Ƙasar nan, amma a haka babu wanda ya taɓa ganin matarsa a Gwabnatance.
Shi kaɗai ne babban ɗan siyasar da na sani a dukkan faɗin Ƙasar nan da yake burin sauyawar rayuwar Ƴaƴan talakawa kamar yadda rayuwar nasa Ƴaƴan take sauyawa cikin rigar ilimin zamani.
Shi kaɗai ne ɗan siyasar da na san yana kishin al'ummar sa wanda sakamakon hakan ake masa kallon mutum mai tsantsar ƙabilanci. Zai iya salwantar da lokacinsa dan ya kankaro darajar mutanensa a idon duniya.
Ba ɗan siyasa bane shi kamar kowani irin ɗan siyasa. Shi ɗan siyasa ne mai sunan ɗan siyasa, dalilin da yasa kenan ya mayar da hankalinsa kacokam kan siyasa saboda fahimtar ta nan ne burinsa na tallafawa al'ummar sa zai tabbata. Da siyasa, ya gina rayuwar Ƴaƴan talakawa da ba za su lissafu ba, ya samarwa da iyaye mata da matasa ƙananan sana'o'in dogaro da kai da har gobe suna cin moriyarsa.
Ga wanda Allah yasa ya taɓa zama dashi zai fahimci cewa Kwankwaso shi ne cikakkiyar ma'anar daraja, domin kuwa duk zaman da za kayi da shi maganarsa ɗaya ce, ci gaban matasa da samarwa iyaye mata sana'o'in dogaro da kai. Bai taɓa maganar ilimi don Ƴaƴan masu hannu da shuni ba, kullum maganarsa akan ilimi yadda ɗan talaka zai zamanto wani shi ma a rayuwarsa domin al'ummar sa ta amfane shi.
Wannan mutum da daraja yake. Shi yasa ban taɓa danasani ko baƙin cikin zamantowa ɗaya daga cikin mabiyansa ba. Zan cigaba da binsa tare da tallafawa dukkan wasu hanyoyin cikar burinsa na kyautata rayuwar ɗan talaka daga nan har zuwa lokacin da Allah zai ƙarɓi numfashina.
0 Comments