k lokacin masu gaskiya sukayi shiru, sai makaryata suke tunanin sune masu gaskiya, amfani da hankali bai kasance kamar gani da ido ba, ta yiwu idanu suyi wa masu su karya, amma hankali baya yaudarar wanda yayi aiki dashi,wasu yan ganganima sun far mana da cewa jagoran Imamu Rabiu Musa Kwankwaso (Radiyallahu Anhu) wai baya zuwa ta'aziyya idan anyi rasuwa, banso nace musu uffan ba, don babu wata hujja da suka dogara da ita, sai molanka sai shaci fadi, wanda kuma sharri ne zalla, don kuwa har ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Ganduje yaje a garin Dawakin Tofa, wanda makiya sukayi amfani da damar wajen kokarin bata masa suna, dukda da dai hakonsu bai cimma ruwa ba.
Ta'aziyya ana yinta ko daga birnin sin ne, yanzu da muke cikin zamani Digitally, wato sai na fahimci wasu suna zuwa gaisuwar mutuwa ne don ace sunje ba don Allah ba, wai har yada hotunan da mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, akeyi ana nuna yaje yiwa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa, amma shi Kwankwaso baije yayi masa gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa ba, to indai don ace anje ne babu lada, wanda baije ba yayi addu'a a inda yake sai yafi wanda yaje samun lada, matukar ya tsarkake niyya.
Gaisuwar mutuwa ba biki bace da za'a ce na yiwa wane nima saiya rama min, wannan ba musulunci bane, kuma wani na iya daukewa wani, musulunci ya bada wannan uzurin, manya manyan jagororinmu dasu akayi jana'izar mai babban daki, anje ta'aziyya kashi kashi, to kuma sai gashi jiya Jagora yaje da kansa yayi ta'aziyya ga sarkin Kano dana Bichi, masu rantsuwar ba zaije ba, sai ku shirya yin kaffara, masu sharri da karya sai ku nemi yafiyarsa.
Mu ajiye wannan sharhin haka, wannan maganar ma Daraja ce a garemu, a damu da cewa Kwankwaso baije gaisuwar mutuwar wane ko wance ba, duk malaman da suka je, da masu mulki, da masu sarauta, da yan kasuwa, da talakawan gari, ba'a gamsu da addu'ar kowa ba, sai Kwankwaso ake jira yazo yayi tasa, lallai wannan Daraja da wasu mutanen suka bamu sai mu gode musu, da addu'ar Allah ya karawa Kwankwaso ingantacciyar lafiya da tsawon rai mai albarka, don a cigaba da damuwa idan baije ta'aziyya ba, mu kuma mu rokeshi ya amsa koken masu koke, su rabauta da karamarsa da suke bukata daga gare shi.
Nasan cewa ko Ganduje aka cewa Kwankwaso baya zuwa gaisuwar mutuwa, zai musanta, saidai kuma idan sabanin zahiri zai fada, don Kwankwaso yaje masa gaisuwar Mahaifiyarsa, shi kuma ya gaza zuwa yiwa Kwankwaso gaisuwar Alhaji Musa Sale, wanda a ranar da ya rasu a ranar Ganduje yabar kasar nan, bayan ya dawo ma, saida ya zauna a Abuja tsawon kusan kwana 5, har Kwankwaso ya koma Abuja bayan anyi addu'ar bakwai, amma Ganduje baije ba, duk bamu ce Ganduje bai kyauta ba, mu kuma da yake namu jagoran mai Daraja ne, kwadayin zuwansa ta'aziyya ake, Allah mungode ma.
Yunkurin zubar da mutuncin wani babu gaira babu dalili, ko kulla makirci don raba wata alaka ko cusa tsanarsa a zuciyoyin al'umma zalunci ne, Allah shine yake daukaka bawansa ko kanskantar dashi, wanda kuma duk ya dauki aniyar kaskantar da wani to tabbas ya sabawa Allah, kuma ya tunkari halaka, daga karshe reshe ne zai juye da mujiya ko kuma abinda yafi karfi ya gagare shi. Jagora ka kyalesu da halinsu, domin baka damuwa da ramuwa akan cutarwarsu, hakanne ya siffanta raunanan dabi'unsu, da so samu ne ma, ka cigaba da kyautata musu, da sannu zaka riski sakamakon jarumtarka, a lokacin da zasu gane illar rauninsu.
0 Comments