Aiki: Shugabanni basu da damar cutar da wadanda ke da hakki akansu

 



Bisa yadda kundin tsarin mulkin Nigeria ya bada dama, shine gwamnatin tarayya zata dinga bawa jihoji kudi dukkan watan Duniya, domin tasarrafinsu akan gudanarwa, ciki harda biyan ma'aikatan gwamnati albashinsu wanda hakkinsu ne da ya zama tilas a biya su, ba alfarma bace ko taimako, wannan tasa shugabanni masu adalci da sanin ya kamata, suke himmatuwa wajen ganin sun fita hakkin mutanen dake karkashinsu.


An zabi Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin gwamnan jihar Kano karon farko a shekarar 1999, mutumin da ya samu kalubale akan harkar gudanarwar mulki, kasancewar ya karbi mulki a hannun soja, Col. Aminu Isah Kwantagora (Allah yaji kansa da rahama), ya tarar ma'aikatan gwamnati suna karbar kudin albashi a hannu (Abinda ake kira table payment), wanda hakan yana kawo rudani, ta yadda ma'aikaci zai tarar da kudinsa basu kai ba a wasu lokutan, da sauran matsaloli, hakan tasa ya mayar da tsarin biyan albashi zuwa banki (E-payment), Kwankwaso ne ya yiwa ma'aikata wannan gatan.


A 2011 bayan ya dawo gwamnan jihar Kano karo na biyu, Kwankwaso ya samar da asusun bai daya (T.S.A), wanda dukkan kudaden gwamnati na haraji da sauransu suke zuwa cikinsa kai tsaye, sabanin a baya kowacce ma'aikata ko hukuma tana da nata asusun, shi yasa kudaden gwamnati suka dinga zurarewa, wannan ta bawa gwamnatin Kwankwaso damar biyan albashi a dukkan 25 ga wata, tare da bada kudin Gero da watan Ramadan, da kuma kudin Rago lokacin babbar Sallah, musamman ga kananan ma'aika don suyi walwala kamar manyan ma'aikata.


Kwankwaso bai tsaya anan ba, ya shigo da tsarin bada rancen abin hawa ga ma'aikata, domin su biya sannu a hankali ba tare da kudin ruwa ba, tare da inganta musu wuraren aikinsu, kama daga gyara musu ofisoshi, da sauransu, wannan ta bashi damar samun nasara a mulkinsa ta bangaren ma'aikata, kowa ya dawo zuwa wajen aikinsa akan lokaci ya tashi akan lokaci, domin dukkan bukatunsa ana biya masa, musamman albashi da yake abin dogaro ga ma'aikaci.


Bugu da kari, Kwankwaso, ya bada gudummawa ta motoci a ma'aikatun gwamnati da dama dake jihar Kano, domin saukaka harkokin sufuri idan bukatar hakan ta taso, ya kuma bada aiki bisa cancanta ba tare da shigar da siyasa ba, domin ko lokacin da gwamnatin tarayya ta bada umarnin korar ma'aikata malaman makarantun firamare da basu da shaidar ilimi koyarwa (NCE), shine gwamnan da yaki amincewa da haka, sai ya bullo da wani yanayi da ake kira (MAJA), malaman firamare ne suke zuwa karatu a kwalejojin ilimi na tarayya dana jiha a lokacin da akayi hutun makaranta suna karatun NCE, kuma a kyauta domin su samu shaidar kammalawa ba tare da sun rasa aikinsu.


Zamu dauki lokaci mai tsayi wajen bayyana tagomashin da ma'aikata suka samu daga gwamnatin Kwankwasiyya a jihar Kano, domin gwamna Kwankwaso da kansa ba sako ba, yakam ziyarci ma'aikatun gwamnati bagatatan, irin ziyarar da ake cewa ziyarar bazata, duk domin ya tabbatar da cewa an inganta harkokin aikin gwamati, har ila yau ya bawa kungoyin kwadago damar gudanar da tsarinsu da kansu, ba tare ya shiga ciki yayi musu katsalandan ba, abinda ya bashi nasarar kyautata alaka tsakaninsa dasu.


Kash! Yanzu kam a iya cewa hannun agogo ya dawo baya karkashin mulkin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan da ya bugi kirjin cewa zai aiwatar da tsarin N30,000 a matsayin mafi karancin albashi, harma ya kara da wata N600 duk domin yaja hankalin ma'aikata, sai gashi ya gagara cimma wancan batu nasa, ya saka zabira yana yankar kudaden albashin ma'aikata, zabirar da kaifinta ya zarce lokaci guda, tana aiki a duk lokacin da ta bukata, wanda babu ranar biyan ma'aika wannan hakki nasu, ga kuma shigar da siyasa cikin aiki, don anji shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, yana fadin cewa sai mutum ya nuna katin shaidar zama dan jam'iyyarsu sannan zasu dauke shi a aiki.


Mafi akasarin ma'aikata a jihar Kano, sunfi gamsuwa da cewa hakkinsu na cire wasu sassa na albashinsu bazai dawo ba, muradinsu shine a dakata daga yankar musu, a kuma dawo da tsarin biyansu albashi akan lokaci kamar yadda gwamnatin Kwankwasiyya ta aiwatar, sabanin gwamnatin Ganduje da wani watam ma saiya mutu sabo ya kama, shima sai yayi kwanaki sannan a biya, hakan tasa yanzu ma'aikata a jihar Kano basu da cikakken masaniya akan nawa ne ainihin albashinsu, sai abinda suka gani kawai.


Duba da irin gudummawa wajen inganta harkar aikin gwamnati da gwamnatin Kwankwasiyya tayi a jihar Kano, muna amfani da wannan rana domin jajanta ma'aikatan wannan jiha, bisa tsarin kama karya da suke fuskanta daga gwamnati mai ci, kuma wanda ya fito ya fada ma yayi laifi, muna basu hakuri akan haka, su kara juriya zuwa wani lokaci anan gaba da muke fatan Allah zai dawo da gwamnatin Kwankwasiyya a jihar Kano, domin cigaba da inganta musu harkokinsu na aiki. 

Ranar Maaikata Ta Duniya

International Workers Day 



Post a Comment

0 Comments