Lalacewar da ta sa mu Buhari abin kunya ce gareshi, babban abin kunya din shine, yadda farkon sa ya zama wanda yafi kowa farin jini a tarihin shugabancin wannan kasa, karshensa kuma ya zama wanda yafi kowa bakin jini.
Bamu taba jin labarin shugaban kasar da aka bi shi har wata kasa a kofar gidan da yake kwana ba, aka zunduma masa ashariya aka ci mutuncinsa ba, sai Buhari. Abin mamaki kuma a kasar da iya gudun hijirar masu mulki a can ne duk wani gudun muntsirar su yake. Idan har Buhari bai tsira a London ba, dan Allah a ina zai sa mu kwanciyar hankali kuma?
A kasar ka tun ba aje ko ina ba an tsine maka, a garin haihuwarka ana tsitssine maka, a yankin ka har naushi aka kai maka, sannan kuma a kasar da kake tinkahon duk wani karfi naka yana can, a can ma an bika da yeho.
Idan da ace azzaluman shuwagabanni suna daukar darasi da daga Buhari sun shafa wa kansu lafiya, ba zato ba tsammani shi da masoyansa babu wanda ya tsammaci wannan yanayin zai zo haka. Zalunci na da iyaka, Buhari wuyansa a daure yake da jinanen bayin Allah da basu ji basu gani ba, kuma tabbas sakamakon wannan zaluncin ne ya dabaibaye mulkinsa da rayuwarsa. Allah ka yi mana kyakkyawan karshe, ka yafe mana laifukanmu, kasa mu gama da duniyar nan lafiya.
0 Comments