Ba Kwadayin Naira Muke Ba, Mu Saidai 'Yancin Talakka!

  



Shahararren Dan Siyasa A Najeriya, Wanda Yake Da Manufar Siyasa Ta Ganin Talaka Ya Samu 'Yanci, Mutunci Da Kuma Raba Dai-Dai Tsakanin Al'umma, Wannan Itace Manufarsa Har Yabar Duniya A Lokacin Da Yake Dan Shekara 63 Da Haihuwa, Yayi Rayuwarsa Ta Duniya Daga (1920 Zuwa April 17, 1983), Ya Zama Garkuwar Talakawa A Lokacin Da Ya Samar Da NEPU A Jamhuriyya Ta Farko, Da Kuma Jam'iyyar PRP A Jamhuriyya Ta Biyu. 


A Zamanin Yanzu An Samu Dan Siyasa Daya Tilo, Wanda Yake Dukkan Ra'ayi Da Manufofin Marigayi Malam Aminu Kano. Kamar Yadda Malam Aminu Kano Ya Ajiye Aikinsa Na Gwamnati, Domin Bada Gudummawa Wajen Cigaban Kasa Da Jin Dadin Rayuwar Talaka, Haka Shima Jagora Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Ya Ajiye Aikinsa Na Gwamnati Domin Fafufukar Cigaban Al'umma. 


Malam Aminu Kano (Allah Ya Kyautata Makwanci) Ya Kasance Dan Siyasa Mai Karfin Iko, Wanda Yake Tsayawa Mutum Yaci Zabe, Kuma Yake Kin Mara Masa Baya Ya Fadi Zabe, Domin Talakawa Sun Yarda Dashi, Sun Sani Bazai Kawo Musu Abin Cutarwa Ba. Ya Samu Nasarori Ta Hanyar Bawa Matasa Dama A Jam'iyya Da Sha'anin Mulki, A Lokacin Aka Bawa Sule Lamido Daga Jigawa, Shugaban Matasan Jam'iyyar PRP Na Kasa Baki Daya, Daga Baya Aka Tsaida Shi Takarar Dan Majalisar Wakilai Ta Kasa Karkashin Jam'iyyar PRP A Shekarar 1979, Kuma Yayi Nasarar Zama Wakilin Karamar Hukumar Birnin Kudu. 


A Tarihin Musulunci, Matasa Sun Bada Gudummawa Matukar Gaske Wajen Kafuwarsa. Haka Jagora Kwankwaso Ya Kasance Mai Shigar Da Matasa Matsayi Daban Daban Na Siyasa. Kuma Ya Dauki Salon Sanya Tufafi Irinna Malam Aminu Kano, Fararen Kaya Da Kuma Jar Hula. Kokarin Samar Da Ilimi Ga Al'umma Wannan Dashi Kwankwaso Yafi Shahara, Wanda Kuma Duk Al'ummar Dake Bukatar Cigaba, To Tabbas Ya Kasance Suna Da Ilimi. 


A Wannan Rana Ne, Marigayi Malam Aminu Kano, Ya Cika Shekaru 38 Da Komawa Ga Mahaliccinsa, Ubangiji Allah Ya Kyautata Makwancinsa Yayi Masa Rahama, Idan Tamu Tazo Yasa Mu Cika Dakyau Da Imani. Jagora Kwankwaso Allah Ya Kara Masa Lafiya, Ya Dorashi Akan Makiyansa, Ya Bashi Nasara Akan Dukkan Abinda Ya Sanya Gaba, Tare Damu Baki Daya. 


Post a Comment

0 Comments