Kwankwasiyya Ta Kammala Kashin Farko Na Horar Da Mambobinta Akan Social Media


Kungiyar Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Ta Bayyana Jin Dadinta Da Kuma Farin Ciki Bisa Kammala Bada Horo Ga Wasu Daga Mambobin Kungiyar A Matakin Kananan Hukumomi Na Jihar Kano, Wanda Kusan Mutane 60 Suka Samu Horo Na Musamman, Akan Yadda Zasu Wallafa Rubutu Mai Tasiri A Kafafen Sadarwa Na Zamani, Da Kuma Yadda Zasu Samar Da Cikakken Tsaro Akan Asusunsu Na Social Media, Harma Da Dabarun Gudanar Da Yakin Neman Zabe A Kafafen Sadarwa Na Zamani. 


Comr. Abdullahi Ghali Basaf, Shine Shugaban Kungiyar Na Kasa Baki Daya, Yayi Kira Ga Wadanda Suka Samu Nasarar Samun Wannan Horo, Kan Cewa Su Dage Wajen Ganin Cigaban Kwankwasiyya A Kowanne Mataki, Su Kuma Guji Shiga Duk Wani Sha'ani Dazai Kawo Rashin Fahimta, Su Himmatu Wajen Isar Da Sakonni Da Zasu Kara Karfafa Kwankwasiyya A Nigeria, Da Duniya Baki Daya. 


A Nasa Bangaren, Shugaban Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Reshen Jihar Kano, Amir Abdullahi Kima, Ya Bayyana Jin Dadinsa Da Wannan Horo Da Mambobinsa Suka Samu, Ya Kuma Bukataci Suyi Amfani Da Abinda Aka Koya Musu Wajen Aika Sakonni, Salon Sakon Duk Wani Dan Kwankwasiyya Reporters, Ya Kasance Ya Bambanta Dana Kowa, Wajen Sahihanci, Inganci, Da Kuma Cika. Ya Kuma Bukaci Su Cigaba Da Wayar Dakan Sauran Mambobi, Kafin Horon Yazo Kansu. 


Har Ila Yau, Shima Wanda Jagoranci Bada Horon, Abubakar Lecturer, Yayi Godiya Da Fatan Alheri Ga Wadanda Suka Rabauta Da Wannan Horo, Musamman Hadin Kai Da Suka Bashi Har Aka Samu Nasarar Aiwatarwa Cikin Makonni Biyu, Da Kuma Kira A Garesu Kan Suyi Kokari Wajen Tabbatar Da Abinda Suka Koya A Aikace, Ya Kuma Tabbatar Da Cewa, Wannan Shine Karon Farko, Za'a Cigaba Da Wannan Training Da Yardar Allah. 


A Madadin Shugabancin Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Na Taya Murna Ga Dukkan Wadanda Suka Samu Nasarar Wannan Horo.

Post a Comment

0 Comments