Tasiri: Kwankwaso Ya Kere Sa'a A Da'irar Siyasar Nigeria, Karanta Kayi Alkalanci

 





Bayan Gwagwarmayar Karatu, Ya Fara Aikin Gwamnati A Hukumar Samar Da Ruwan Sha Ta Jihar Kano (WRECA), Cikin Shekarar 1975, Haka Ya Shafe Tsawon Shekaru 17 Cikin Wannan Aiki, Ya Rike Mukamai Daban Daban, Har Saida Yakai Matsayin Babban Injiniya, Kafin Daga Bisani Ya Ajiye Aikinsa Ya Kuma Shiga Da'irar Siyasa A Shekarar 1992, Cikin Jam'iyyar SDP, Karkashin Jagorancin General Shehu Yar'adua, Ya Hadu Da Wasu Yan Siyasa, Irinsu Magaji Abdullahi, Babagana Kingibe, Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Tony Anenih, Chuba Okadigbo, Abdullahi Aliyu Sumaila, Lamidi Adedibu Da Sauransu. 


Abinka Da Dan Sa'a, Cikin Shekarar 1992 Aka Zabeshi A Matsayin Dan Majalisar Wakilai Ta Kasa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Madobi Daga Jihar Kano, Harma Ya Rike Mukamin Mataimakin Shugaban Majalisa, Daga Nan Siyasarsa Ta Koma A Matakin Kasa, Domin Cikin Shekarar 1995 Aka Zabeshi Domin Ya Wakilci Jihar Kano A Babban Taron Samar Da Kundin Tsarin Mulkin Nigeria, Karkashin Tafiyar Siyasarsu Ta Democratic Movement, Kafin Daga Bisani Ya Shiga Cikin Jam'iyyar DPN Mai Take "Alheri".


Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Shiga Jam'iyyar PDP Power, A Shekarar Ta Aka Kafata, Wato 1998, Kuma Yana Cikin Mutane Hudu Daga Bangaren Tabo (Receivers), Malam Musa Gwadabe, Sanata Hamisu Musa, Zubairu Dambatta Da Kuma Shi Kwankwaso, Domin Akwai Ragowar Rukunin Gidajen Siyasa Da Suka Shiga PDP A Jihar Kano, Haka Aka Zauna Aka Yarda Kowa Ya Kawo Mutanensa Domin Ayi Shugabancin Jam'iyyar A Jihar Kano, Cikin Sanin Ya Kamata Da Adalci, Kwankwaso Yace Ko A Karamar Hukumarsa Ta Madobi, Ba Zaice A Saka Koda Mutum Daya Ba, Domin Kowa Nasa Ne, Haka Ayi Shugabanci Lafiya Aka Gama Lafiya. 


Bayan Shekara Guda, Kwankwaso Ya Nemi Jam'iyyar PDP Ta Sahale Masa Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Kano A Karkashinta, Cikin Shekarar 1999, Wannan Tasa Jam'iyyar Ta Bada Izinin Ayi Zaben Fidda Gwani Na Cikin Gida (Primary Election), Domin Bayan Kwankwaso Akwai Wasu Da Suke Nema A Basu Wannan Takara, Jam'iyyar Ta Turo Wakiltanta Daga Abuja, Domin Gudanar Da Zaben Fidda Gwani, Tony Momoh A Matsayin Shugaba, Da Sauran Mambobinsa Guda Biyu, Abdullahi Aliyu Sumaila Da Kuma Sanata Bala Tafidan Yauri, Akayi Zabe Kwankwaso Ya Kayar Da Ragowar Yan Takara, Irinsu Alhaji Muntari Zumit, Alhaji Kabiru Rabiu, Da Kuma Abdullahi Umar Ganduje. 


Kwankwaso, Yana Da Wanda Ya Zaba Domin Yi Masa Takarar Mataimaki, Amma Wasu Daga Cikin Dattawan Jam'iyyar A Kano, Suka Tsaya Akan Lallai Sai Abdullahi Umar Ganduje, Dukda Dai Wasu Basu Amince Da Shi Ganduje Din Ba Da Farko, Irinsu Sanata Bello Hayatu Gwarzo, Haka Aka Bawa Wancan Hakuri Aka Dauki Ganduje, Har Allah Ya Bawa Kwankwaso Nasarar Zama Zababben Gwamnan Jihar Kano A 1999, Tsawon Shekaru Hudu Yana Shimfida Ayyukan Alheri A Mulkinsa, Kwatsam Saiga Malam Ibrahim Shekarau Ya Shigo Da Sigar Addini, Hakan Tasa Mutane Suka Amince Masa Da Zaton Addinin Ne A Ransa, Kwankwaso Ya Fadi Zaben Gwamna Karo Na Biyu A 2003, Shekarau Yayi Nasara, Amma Dukda Karfin Iko Nasa, Da Kuma Kasancewarsa Dan Lelen Shugaban Kasa Na Wancan Lokaci, General Obasanjo, Kwankwaso Bai Murde Zaben Ba, Saima Yayi Taron Manema Labarai A Fadar Gwamnati, Ya Bawa Magoya Bayansa Hakuri, A Zauna Lafiya A Karbi Kaddarar Allah, Ya Kuma Kwashi Tawagar Gwamnatinsa, Mataimakinsa, Sakataren Gwamnati Da Sauran Kwamishinoni, Zuwa Gidan Shekarau Akayi Masa Murna Da Addu'ar Samun Nasarar Mulki. 


A 2003, Shugaban Kasa Obasanjo Ya Bawa Kwankwaso Mukamin Ministan Tsaro, Bawan Karewar Wa'adin Wanda Yake Kai Daga 1999 Zuwa 2003, Mai Suna Theophilus Danjuma, Har Zuwa 2006 Da Kwankwaso Ya Dawo Domin Sake Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Kano, Dukda Tuhume-Tuhume Da Yake Fuskanta Daga Gwamnati Shekarau, Shari'a Kala-Kala A Kotuna Da Sauran Hukumomi, Har Zuwa Lokacin Da Akayi Masa White Paper (Wata Takarda Da Ake Bawa Yan Siyasa, Sai Sunyi Tsawo Shekara 10 Basu Tsaya Takara Ko An Basu Mukamin Siyasa Ba), Kawai Saboda Kiyayya, Hakan Tasa Ya Tsayar Da Alhaji Ahmad Garba Bichi A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano, Karkashin Inuwar Jam'iyyar PDP Mai Alamar Laima, Da Dan Takarar Mataimakin Gwamna Engr. Abubakar Jibril Mohammed, Daga Karamar Hukumar Gwale, A Zaben 2007.


Jam'iyya Mai Mulki A Wancan Lokaci Ta ANPP Tayi Amfani Da Dabaru Na Ganin PDP Batayi Nasara Ba, Amma Dukda Haka Tazarar Kuri'un Bata Kadan Ce, ANPP Ta Samu 671,184, Yayin Da PDP Ta Samu 629,868, Sai Kuma Ragowar Yan Takara Irinsu Bala kosawa Na Jam'iyyar NDP, Umar Y. Dan Hassan Na Jam'iyyar PSP, Usman Sule Na Jam'iyyar AC, Hamisu Lamido L. Iyantama, Da Sauransu, Hakan Tasa PDP Ta Garzaya Kotu Nemawa Al'ummar Jihar Kano Hakkinsu, Amma Aka Gagara Bawa Al'umma Zabinsu, Tafe Tafe Har Majalisar Tarayya Da Kotu Suke Soke Batun White Paper. 


Majalisar Kasa Tayi Doka, Tare Da Aikawa Dukkan Jihohin Nigeria, Jihohi 24 Kawai Majalisar Take Bukatar Su Amince, Shikenan Dokar Janye White Paper Ta Tabbata, Allah Da Ikonsa Dukkan Jihohin Nigeria 36, Guda 35 Sun Yarda A Janye, Guda Daya Ce Kawai Bata Amince Ba, Itace Jihar Kano, Kuma Saboda Rabiu Musa Kwankwaso, Daga Nan Shugaban Kasa Umar Musa Yar'adua Ya Bashi Mukamin Mamba A Hukumar Kula Da Yankin Niger Delta, Kafin Daga Bisani Ya Kaiwa Shugaban Kasa Good luck Jonathan Takardar Ajiye Aikinsa Bisa Radin Kansa (Bayan Yar'adua Ya Rasu), Dukda Cewa Shugaban Kasa Baiji Dadi Ba, Amma Kwankwaso Ya Shaida Masa Cewa Bazai Iya Zama Ba, Saboda Rashawa Da Tayi Kamari A Hukumar, Sai Shugaban Kasa Ya Bashi Damar Ya Kawo Wani A Madadinsa, Kuma Ya Bayar, Haka Yayi Kamshin Dangoma A 2011 (Dawo Dawo),  Kwankwaso Ya Dawo Kano A Matsayin Dan Takarar Gwamna A Jam'iyyar PDP. 


Bayan Anyi Zabe Yayi Nasarar Zama Gwamnan Kano Karo Na Biyu A 2011, Bai Tsaya Batun Ramuwar Gayya Ba, Sai Kawai Ya Himmatu Akan Dora Jihar Kano Kan Cigaba Mai Dorewa, Musamman Bangaren Ilimi, Har Zuwa 2014 Da Ya Shiga Jam'iyyar APC, Biyo Bayan Kasawar Gwamnatin Tarayya Ta PDP, Musamman Matsalar Tsaro, Da Kyakykyawar Niyyar A Dora Nigeria Kan Turba Mai Kyau Karkashin Jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Har Zuwa 2015 Da Aka Tursasa Kwankwaso Ya Tsaya Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A APC, Domin Buhari Yaci Zabe, Tunda Dai Zaben Shugaban Kasa Dana Sanata A Rana Guda Akeyi, Amma Buhari Ya Watsawa Al'umma Kasa A Ido, Dukkan Alkawuran Da Yayi Ya Gaza Cikawa, Wannan Tasa Kwankwaso Ya Yanke Shawarar Ficewa Daga APC A 2018, Harma Buhari Da Shugaban APC Na Kasa, Adams Oshimhole, Suka Gayyaci Kwankwaso Zuwa Villa, Dayi Masa Danna Kirji, Kada Ya Fice Daga Jam'iyyar, Zasu Bashi Takararsa Ta Sanata, Amma Kwankwaso Yayi Watsi Da Tayin, Domin Shi Ba Gafiya Tsira Dana Bakinki Bane, Makomar Mutanensa Ce Tafi Damunsa, Ba Kamar Shekarau Ba, Wanda Shi Kadai APC Ta Bawa Takarar Sanata, Mutanensa Kuwa Koda Shugaban Party Na Chapter Ba Wanda Ya Samu, Bukatarsa Ce Kawai Ta Biya. Shi Yasa Ko Zaben 2019, Kwankwaso Bai Shiga Kowanne Irin Zabe A Matsayin Dan Takara Ba, Tunda Ya Rasa Tikitin Takarar Shugaban Kasa A Jam'iyyar PDP. 


A 2015 Kwankwaso Ya Tsayar Da Mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje, A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano Karkashin Jam'iyyar APC, Mutanen Kano Suka Zabeshi Da Alkawarin Zai Dora Akan Dukkan Ayyukan Alherin Da Kwankwaso Yayi, Bayan Yahau Ya Shaida Musu Cewa Dama Can Diddike, Sanda Da Likimo Yake, Amma Shi Baya Kwankwasiyya, Wannan Yasa Al'ummar Jihar Kano Sukayi Watsi Da Tsarin Tafiyarsa, Har Lokacin Da Kwankwaso Ya Tsayar Da Engr. Abba Kabir Yusuf A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano A Jam'iyyar PDP A Zaben 2019, Suka Lallasa Gwamna Ganduje, Sai 'Yan Tsirari Da Suka Bashi Kuri'u 987,819, Dukda Cewa Yace Ya Samu Kuri'u Kusan Miliyan Biyu A Zaben Fidda Gwani Na Jam'iyyar Tasu Ta APC, Yayin Da Aka Zabi Abba Kabir Yusuf Da Kuri'u 1,014,474 Wanda Hakan Ya Nuna Cewa Shine Yayi Nasara, Kafin Daga Bisani Ayi Taron Dangi Da Sunan Inconclusive A Yiwa Mutanen Kano Fashin Zabe, Har INEC Ta Bayyana Ganduje A Matsayin Wanda Ta Bawa Nasara. 


Bayan Zuwa Kotu Har Hawa Uku, Sun Sake Tabbatar Da Ganduje A Matsayin Wanda Yayi Nasara, Dukda Tarin Shaidu Da Hujjoji Da Aka Gabatar Da Suke Nuna Cewa Ganduje Baici Sahihin Zabe Ba, Daga Ganduje Ya Cigaba Da Kalamai Daban Daban, Harma Yana Cewa Wai Ya Yiwa Kwankwaso Ritaya Daga Siyasa, Sai Gashi Kuma Kullum Bashi Da Abin Ambato Da Yake Masa Barazana Kamar Kwankwaso, Gashi Ya Dakko Tsari Na Yunkurin Rusa Aiki Da Kwankwaso Yayi A Jihar Kano, Wanda Kuma Bazai Taba Iya Dusashe Hasken Kwankwaso Ba, Domin Yayi Dashen Da Har Abada Ba Za'a Manta Dashi Ba, Shine Dashen Ilimi, Da Inganta Rayuwar Dan Adam, A Ginashi Ya Zama Wani, Harma Ya Janyo Wasu Shima, Suma Su Janyo Wasu, Haka Haka Kamar Matattakalar Bene. 


A Matsayina Na Abubakar Lecturer, Dan Kwankwasiyya Kuma Ma'aikaci A Sashen Gidan Talabijin Na Kwankwasiyya Reporters, Nayi Wannan Nazari Musamman Domin Bayyana Tasirinsa A Da'irar Siyasa, Shine Yabar Gwamna Tsawon Shekaru Takwas, Kuma Ya Dawo Karba, Wasu Suna Ganin Duk Wanda Yabar Gwamna Baya Dawowa, Shi Yasa Wasu Suke Nacewa Sai Sun Zarce, Shine Wanda Yake Fita Daga Jam'iyya Mai Mulki Ya Shiga Mara Mulki, Duk Domin Al'ummarsa, A Yanzu Dai Babu Wani Mai Tarihin Siyasa Mai Cike Da Tarnaki Da Nasarori Irinsa Ba, Munga Yadda Wasu Aka Shafe Tarihinsu, Wanda Abinda Ya Samesu Bai Kai Rabin Rabin Nasa Ba. 


Idan Na Samu Lokaci, Zan Sake Wani Nazarin Na Musamman Insha Allah. 



Post a Comment

0 Comments