Shugaban Kwankwasiyya Reporters Na Jihar Kaduna, Ya Angonce

 

Jiya Asabar 20/02/2021, Yayin Da Wakilcin Kungiyar Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Suka Halarci Garin Zaria Dake Jihar Kaduna, Domin Taya Murna Ga Shugaban Kungiyar Ta Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Reshen Jihar Kaduna, Comr. Sani Saeed Altukry, Wanda Aka Daura Aurensa Jiya A Babban Masallacin Juma'a Na Bomo Dake Garin Zaria. 


Tawagar Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Na Kasa Baki Daya, Comr. Abdullahi Ghali Basaf, Dattijo Kuma Uba A Kungiyar, Alhaji Jafar Mariri, Shugaban Kungiyar Na Shiyyar Jihohin Arewa Maso Yamma, Comr. Yusuf Dankanjiba, Mataimakin Shugaban Kungiyar Na Jihar Kano, Auwal Sani Rogo, Shugaban Kungiyar Na Shiyyar Kano Ta Tsakiya, Kabiru Ali Dankabido, Da Kuma Abubakar Lecturer, Ne Suka Wakilci Dukkan Shugabanni Da Sauran Mambobi. 


Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Tayi Addu'a Ubangiji Allah Ya Sanya Alheri A Wannan Aure, Ya Basu Zaman Lafiya Mai Dorewa, Tare Da Zuri'a Tagari, Dashi Da Amaryarsa. Ameen. 



Post a Comment

0 Comments