Duba Da Dabi'unsa Nagartattu, Alhaji Yahaya Musa Kwankwaso, Ya Cancanci Nadin Da Akayi Masa A Matsayin Sabon Dagachin Garin Kwankwaso, Sakamakon 'Daga Likkafar Tsohon Dagachin Kwankwaso, Alhaji Sale Musa Sale Kwankwaso (Baaba Kwankwaso), Zuwa Hakimin Madobi Da Masarautar Karaye Tayi, Biyo Bayan Rasuwar Hakimin Madobi, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.
Alhaji Yahaya Musa Kwankwaso, Dan Uwane Ga Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Mutum Ne Mai Kyakykyawar Mu'amala Tsakaninsa Da Al'ummar Da Yake Rayuwa Acikinsu, Wanda Yake Burin Ganin An Samar Da Cigaba Mai Dorewa A Jihar Kano, Arewa Da Nigeria Baki Daya.
A Madadin Shugabanni Da Dukkan Mambobin Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Muna Mika Sakon Taya Murna A Gareshi, Da Addu'ar Ubangiji Allah Ya Sanya Alheri Da Albarka, Yayi Masa Jangora, Ya Bashi Damar Adalci A Tsakanin Al'ummar Da Yake Mulka, Ya Kuma Tsareshi Daga Dukkan Sharri, Duk Wata Nasara Da Allah Yake Bawa Mai Mulki, Muna Fatan Allah Ya Bashi.
0 Comments