Daga: Khadija Garba Sanusi
Kamfanonin Dangote Group, BUA Group,Tiamin Rice da Umza Rice zasu dauki Daliban Kwankwasiyya su 370 aiki, kamfanonin sun bayyana ahakane a Wani Taron nemawa Daliban Kwankwasiyya aiki da akayi Yau Asabar 27/2/2021 gidan jagoran Kwankwasiyya Na Duniya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso dake Miller Road Bompai a Birnin kano.
A jawabinsa Da yagabatar a Taron wakilin Alhaji Aliko Dangote Eng Mansur Ahamad tsohon Shugaban Kamfanin Mai Na kasa NNPC yace yazama wajibi a yabawa Sanata Kwankwaso Bisa wannan namijin Kokari da yayi Na daukar nauyin yayan talakawa Har su 370 zuwa kasashen waje karatu Duk da cewar Babu Gwamnati a hanunsa Yau gashi sun kammala sun dawo cikin Nasara yazama dole amatsayinsu Na Yan kasuwa masu Kamfanoni auto hobbasa Domin ganin sun dauki wadannan Dalibai aiki.
Shima a nasa Jawabin wakilin Alhaji Abdussamad isiyaka Rabi'u Shugaban Kamfanin Bua wato Alhaji Idi Hong tsohon Minista a Gwamnatin PDP yace zassu dauki wasu Daga cikin Daliban aiki.
Tunda da farko Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa Daya Daga cikin Jami'o'in wato Mewar University dake India ta dauki mutum 13 Daga cikin wadannan Dalibai aikin Koyarwa a Jami'ar, sannan Kwankwaso ya godewa Allah da ya bashi wannan dama ta taimakawa marassa karfi yayan talakawa Domin Zu zama wasu a Duniya.
Shugaban Majalisar Malamai Na Jihar Kano Mallam Ibraheem Khalil shima yace dole wadannan Dalibai su godewa Kwankwaso da Al'ummar Jihar Kano Bisa zabar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zama Gwamnan Kano Wanda Hakan ce ta bashi damar aiwatar da wadannan abubuwa Na Alheri a Jihar Kano da Najeriya.
0 Comments