Sashen Gidan Talabijin Na Kwankwasiyya Reporters, Wanda Yake Kawo Muku Shirin Kacici Kacicin Kwankwasiyya, Da Misalin Karfe 8:00pm Na Dukkan Ranar Juma'a, Kai Tsaye (Live Audio) A Shafinmu Na Kwankwasiyya Reporters, Ya Karbi Bakuncin Tsohuwar Kwamishinar Yada Labarai Ta Jihar Kano, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko.
Tsohuwar Kwamishinar, Tazo Wannan Gida Ne, A Matsayin Rakiya Da Ta Yiwa Usaini Muhammad Garko, Wanda Ya Samu Nasarar Samun Sabuwar Atamfa, Cikin Shirinmu Na Kacici Kacicin Kwankwasiyya, Da Ya Gabata, A Matsayinta Na Jigo A Tafiyar Kwankwasiyya A Karamar Hukumar Garko Da Jihar Kano Baki Daya.
Hajiya Ladidi, Wacce Ta Rike Mukamin Kwamishinar Yada Labarai A Zamanin Mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso A Jihar Kano, Ta Yaba Tare Da Jinjina Ga Kwankwasiyya Reporters TV, Bisa Kara Karfin Gwiwa Da Suke A Tsakanin Yan Kwankwasiyya, Musamman Shirin Kacici Kacicin Kwankwasiyya, Da Ake Gabatarwa, Wanda Yake Kara Kaimu A Tsakanin Yan Kwankwasiyya.
0 Comments