Dan Majalisar Dokokin Jihar Kano Mai Wakiltar Karamar Hukumar Fagge, Hon. Tukur Muhammad Fagge, Ya Jagoranci Bude Gida Mai Dakunan Kwana, Wanda Ya Kama Haya A Garin Wudil, Domin Dalibai Yan Asalin Karamar Hukumar Fagge, Da Suke Karatu A Jami'ar Kimiyya Da Fasaha Dake Garin Wudil (KUST).
Kamar Yadda Kowa Ya Sani, Ilimi Shine Ginshiki A Tsarin Tafiyar Kwankwasiyya, Wanda Ita Kanta Makarantar Ta Samu Ne A Gwamnatin Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Daga 1999 Zuwa 2003, A Garin Wudil Dake Jihar Kano, Domin Bunkasa Harkokin Ilimi, Da Samun Yawaitar Guraben Karatu Ga Dalibai A Ciki Da Wajen Jihar Kano.
Karamar Hukumar Fagge, Guda Ce Cikin Kananan Hukumomin Dake Kwaryar Birnin Kano, Wanda Take Da Nisan A Kalla Kilometer 60 Zuwa Karamar Hukumar Wudil, Zuwa Da Dawowa Kullum, Zai Zama Takura Ga Dalibai, Amma Kwanansu Acan Zai Sama Musu Sauki Na Zirga Zirga, Da Kuma Tattalin Arziki, Wannan Tasa Dan Majalisa Ya Gwangwajesu Da Wannan Gida.
0 Comments