Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, kuma shugaban kwamitin janyo bututun iskar gas na jihar Kano, Engr. Muaz Magaji Dan Sarauniya, ya bayyana kalaman shugaban rikon jam'iyyarsu ta APC, Alhaji Abdullahi Abbas, wanda yace ko aikin gwamnati kake nema a Kano, to dole ka mallaki katin jam'iyyar APC, a matsayin kalaman jahilci da rashin sanin ya kamata.
Abdullahi Abbas, yayi wancan jawabi ne yayin taron kwamitin rigistar sabunta katin shaidar zama dan jam'iyyar APC a jihar Kano, wanda ya gargadu ma'aikatan gwamnati da su shiga APC ko kuma a janye musu dukkan wata dama, harma ya bukaci gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da kada ya bawa kowa aikin gwamnati, sai wanda yake da katin shaidar zama dan jam'iyyar APC.
Kalaman sun jawo cece-kuce tsakanin mutane, ciki harda Engr. Muaz Magaji, wanda yake ganin kalaman basu dace da shugaba ba a tsarin damokoradiyya, ballantana ace shugaba a jiha kamar Kano, domin ita gwamnati bayan zabe ta kowa ce, harda yan adawa, kuma akwai miliyoyin yan kasa da basa kowacce jam'iyya, saboda haka yake ganin wannan kalaman sunfi kama da jahilci.
‘’Sam Abdullahi Abbas, bai dace ya zama shugaba a siyasa ba, kullum yana kara mana kiyayya ne ba soyayya ba, maganar gaskiya itace lokaci yayi da ya kamata a sallameshi ya kama wani aikin can dazai kasaitarsa ba tare da yayi mana barin tafiya ba, don mu bama masa kyashi. Idan har mukai shiru da ire iren wannan katobarar, kanawa ba zasu ce damu komai ba, amma ta ciki na ciki, sai ranar Alkalanci, zaben 2019 ma darasi ne." ― Inji Muaz Magaji
1 Comments
Gaskiya abdullahi Abbas babban jahiline
ReplyDelete