Yayin da aikin gadar Kofar Nasarawa yayi nisa, gwamnan jihar Kano (2011-2015) Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, tare da rakiyar mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje na jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, shugaban hukumar KAROTA, Engr. Muhammad Diggol, Dr. Abubakar Nuhu Danburam, da sauran tawagar gwamnati, yayin ziyarar ganin yadda aikin yake tafiya.
An dauki wannan hotuna cikin dare, domin mafi akasari da daddare yake zuwa duba irin wadannan ayyuka, lokacin babu cinkoso, domin ya kalli aikin yadda ya kamata, kasancewar ya samar da fitilu a manya da kananan titunan cikin birnin Kano, zakayi komai tamkar da rana, domin inganta tsaro a fadin jihar Kano.
Gada ce wacce akayita musamman domin rage cinkoso a mararrabar hanyoyin da ta kunsa, wacce kamfanin da sukayi kwangilar gininta, wato TEC Engineering Company Limited suka bada tabbacinta na shekara 100, duk abinda ya sameta kafin wadannan shekaru, to aje wajensu a tuhumesu, yanzu anci shekaru akalla 6, saura 94.
0 Comments