2023: TSAIDA KWANKWASO TAKARAR SHUGABAN KASA ZAI SA JAMIYYAR PDP TA CINYE ZABENTA A CIKIN RUWAN SANYI.

 



A halin da ake ciki Yanzu, idan ana maganar takarar shugaban kasa na 2023, Jamiyya mai mulki ta APC bata da babban tashin hankali da ya wuce Jamiyyar PDP ta tsaida Engnr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin wanda zai yi mata takara. 


Duba da yadda kullum lissafin siyasa yake tafiya a fadin Nigeria mussamman yankin Arewa, Jamiyyar APC bata da wani babban buri da ya wuce ta mallaki yan siyasa irinsu Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Jagora  Kwankwasiyya Dr Rabiu Musa kwankwaso domin samarwa kanta daraja tare da karbuwa wajen al'umma duk da son zuciyarsu da ki fadi bazai barsu su fito fili su bayyana hakan ba.  


Na tabbata mai karatu zai yadda dani idan yayi la'akari da irin yanayin yan siyasar da jamiyyar APC din ta tara. Mafi yawancinsu zaka ga cewa idan har democradiyyar gaskiya akeyi, toh ba lallai su tsaya da kafarsu ba sukai labari, dan kuwa basu da kowa tare dasu duba da yadda suke tafiyar da irin salon siyasar su ta son zuciya wacce kansu kawai suka sani ba ruwansu da al'umma. Da yawa daga cikinsu sun sami damane, saboda shiga rigar Shugaban kasa mai ci a yanzu Muhammadu Buhari duba da yadda al'umma sukayi mashi zaton alkhairi a baya. Sai dai kuma yanzu labarin ya canza, dan kuwa yanzu babu wani wanda zai yadda ya kara zabar bara gurbi saboda wani duba da yadda a yanzu kwaliyya taki biyan kudin sabulu. 


Wannan dalilin ne yasa duk wani shirye shiryen da Jamiyyar APC takeyi na tunkarar zaben 2023,  bai wuce tunanin wanda zasu kara tsayarwa takara ba kuma ya karbu har sukara darewa kan karagar mulki a shekarar 2023. Wannan babban aiki ne a wajensu, dan kuwa izuwa yanzu sun ruga da sun gane cewa akwai babban kalubale a gabansu mussamman wajen yadda zasu wanke kansu  daga wajen al'ummar Nigeria  duba da yadda suka gaza kawo canjin da sukayiwa alumma  alqawari a baya lokacin da suke neman karbar mulki. 


Izuwa yanzu duk wani dan siyasa dake jamiyyar APC ya riga da yasan babu wani roman baka da zasuyiwa talakan Nigeria ya sake zabar jamiyyar tasu, dan haka duk tunanin su bai wuce suyi tsari ba wanda zasu karbi zaben ta karfin tsiya kamar yadda suka saba a yan shekarun da suka shafe suna mulki. Sai dai kuma yanzu sanin kowa ne ba lalle al'umma sukara yadda ba ayi musu karfa karfa duba da yadda jamiyyar ta APC ta kakaba musu talauci da saka su cikin yanayi mara dadi wanda tarihi ya nuna ba'a taba shiga irinshi ba a tarihin Nigeria. 


Dan haka babban tashin hankalinsu shine, Jamiyyar adawa ta PDP ta tsayar da dan takara wanda al'umma suka gamsu dashi kuma zasu tsaya tsayin daka suga sun kare mashi kuri'a. Wannan ne yasa jamiayyar ta APC a kullum take kallon Tsohon Gwamnan Jihar Kano , Sanata (Dr) Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin babban waigi da zai bata matsala da zummar ya samu damar samun takara dan kuwa yanzu duk wani mai lissafin siyasa a Nigeria ya riga da gamsu dacewa babu wani dan siyasa da yake da yawan magoya baya sama dashi. 


Tarihi ya nuna, abune mai wuya ayi magudin zabe a yanayi irin wanda alumma sukan fito kwansu da kwarkwata su zabi abun da suke son zummar a tsayar musu da wanda suke muradi, dan kuwa babu wanda zai yarda a taba mashi kuri'a.  Duk da anan kusa munga yadda jamiyyar ta APC tayi amfani da karfin gwamnati tayi wani irin mummuna zabe wanda a tarihi magudin zabe na duniya ba'a taba irin shi ba, wato zaben inconclusive na jihar Kano. Wannan bashi yake nuna zasu kara samun damar yin irin wannan aika aikar ba, dan kuwa zaben 2023 zai zamanto daban duba yadda alumma suke daukan alwashi.


Banbancin kwatar zaben inconclusive da Sauran zabuka masu alamar tambaya shine, jamiyyar APC tayi nasarar kwace zaben ne ta karfin tsiya saboda hadin kai da ta samu da wasu mutane wayanda suka munafurcin jamiyyar tasu ta PDP a waccan lokacin saboda biyan bukatarsu da wasu dalilai nasu na son zuciya. Sai dai kuma wannan abunda sukayi babu shakka abune wanda ba lallai ya kara tasiri ba anan gaba, duba da yadda idon al'umma ya bude tare da yadda abun yayi matukar batawa al'umma har yasa suke ikirarin cewa ai yanzu anriga da annuwa wa kurciya baka, nufin nan gaba zasuyi duk mai yi'uwa suga sun kare kansu daga irin waccen ta'asa da akayi musu a zaben 2019 mussamman a zaben jihar Kano jihar da tafi kowacce jiha yawan al'umma a fadin Nigeria. 


Dan haka a kullum muke kira tare da zuburar da babbar Jamiyyar adawa ta PDP, data godewa Allah, sannan kuma ta yi karatun ta natsu, tayi duk mai yi'uwa taga tayi amfani da damar da Allah ya bata a halin da akeciki yanzu, ta ajiye son zuciya , ta baiwa al'umma mafi rinjiye dan takarar da suke muradi domin cimma burin yan kasa tare samun damar karbar mulki daga hannun jamiyya mai mulki ta APC. 


Daga karshe ina fatan Allah ubangiji ya zabawa Nigeria mafi alkhairi, ya bawa Jamiyyar mu ta PDP Nasara, Yayi riko da hannun shuwagabannin mu yayi musu jagora wajen fidda kasar Nigeria daga halin data tsinci kanta mara dadi a hannun Jamiyyar APC. 


Post a Comment

0 Comments