2023: Abdullahi Abbas zai gurfana a gaban sifetan yan sanda

 



Jam'iyyar PDP a jihar Kano, ta rubuta takarda zuwa ga babban sifetan yan sanda na kasa, IGP Mohammed Adamu, ta bukatar ya gurfanar da shugaban rikon jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a gabansa, bisa kalaman tunzura al'umma da yakeyi, wanda zasu iya kawo tashin hankali, kuma barazana ne ga tsaro. 


‘’Kukai farmaki tare da hukunta duk wanda zaiyi satar kuri'a a zaben 2023. Ku dauki hukunci a hannunku babu abinda za'ayi. Na baku umarni ku hukunta duk wanda kuka gani yana kokarin magudi, hukuncina ne, kuma babu abinda zai faru.


‘’Ina kira ga matasanmu na jam'iyya, su adana makamansu a yanzu, kafin lokacin amfaninsu yazo." Sakon Abdullahi Abbas ga mutanen APC, yayin bikin rantsuwa ga shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, wanda aka gudanar ranar juma'a 12/02/2021, a filin wasa na Kano Pillars.


Shehu Wada Sagagi, shine shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kano, yace sun mika takarda ga babban sifetan yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, da sauran hukumomin gwamnati, dukda cewa basuyi mamakin kalaman nasa ba, domin dabi'arsa ce furuci na tunzuri, a cewar Sagagi, kamar yadda Kano Online News ta rawaito, a safiyar wannan rana.


‘’A garemu dai babu inda kalamansa zasuyi mana illa, kuma ba zasu canja mutanen jihar Kano daga zaben abinda yake shine muradinsu ba. Bayan haka kuma ko domin dorewar damokoradiyya, akwai bukatar dole a magance yaduwar irin wadannan kalaman tunzuri, wanda ko a baya bayan nan saida yayi irinsu akan jam'iyyar adawa." ― inji Sagagi


Post a Comment

0 Comments