Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, tsagin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi, tace zata dauki matakin da tace zata dauka matukar dai aka sanya jam'iyyar tasu ta PDP cikin jerin jam'iyyun da zasu shiga zaben kananan hukumomi a jihar Kano, wanda za'a gudanar ranar Asabar mai zuwa, inda tace tuntuni ta sanar da janyewa daga cikin zaben, saboda haka bai kamata hukumar zabe tayi mata tilas ba.
Cikin zantawarsa da manema labarai, Shehu Wada Sagagi, yace bai kamata hukumar zabe ta jihar Kano, ta sanya PDP cikin jerin jam'iyyun da zasu shiga zaben ba, domin wadanda ake magana sun shiga zaben da sunan PDP, tuntuni kotu ta dakatar dasu, ta tabbatar musu basu ne jagororin PDP a Kano ba, haka kuma itama uwar jam'iyya ta kasa, wannan yasa suka kasance halattattun shugabanni da aka zaba babu jimawa, kamar yadda Kano Online News ta rawaito.
Bugu da kari, Sagagi ya zargi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, da shiga sha'anin siyasa, domin a ranar 12 ga watan disamba na 2020 aka zabesu tare da rantsar dasu a matsayin shugabannin PDP a Kano, karkashin jagorancin shugaban kwamitin rikon jam'iyyar, Danladi Abdulhamid, wanda uwar jam'iyya, jami'an tsaro, hukumar zabe ta kasa INEC, da sauran masu ruwa da tsaki suka amince da zaben nasu.
"idan shugaban hukumar zabe ta jihar Kano yana da tantama akan sahihancinmu, to kamata yayi ya rubuta takarda zuwa ga hukumar INEC domin samun sahihai, amma baiyi haka ba, sai yake kokarin nuna mune ba akan dai dai ba, saboda haka tilas mu shigar da kara kotu, akan mai kiran kansa da sunan shugaban jam'iyyar PDP a Kano, da kuma shi shugaban hukumar zabe ta jihar Kano, domin jin shin ya kamata KANSIEC ta karbi sunayen yan takara daga wadanda ba sune halattattu ba." - inji Sagagi
A baya dai, Kano Online News, mun kawo muku yadda shugabancin jam'iyyar PDP tsagin Ambasada Aminu Bashir Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, karkashin jagorancin Mahmina Bako Lamido, ta bada sanarwar shiga zaben, harma ta mika sunayenta ga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), kamar yadda shugaban hukumar zaben Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaidawa manema labarai.
0 Comments