Yanzu Yanzu: wani dan Kwankwasiyya ya takali Abdullahi Abbas

 Yanzu Yanzu: wani dan Kwankwasiyya ya takali Abdullahi Abbas 



Wani matashi dan Kwankwasiyya a jihar Kano, mai suna Abubakar Lecturer, ya bukaci yin muhawara akan harkar ilimi, da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, tsakanin gwamnatin Sanata Rabiu Kwankwaso da kuma ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje.


Matashin ya fara da cewa, ‘’Bansan me Abdullahi Abbas yake ji dashi ba, naji yace wai gwamnatin baya babu abinda ta yiwa ilimi sai gina makarantu na banza.


‘’Banso dai nace masa kon kanzil ba, to amma kalmar BANZA da yayi amfani da ita wajen alakanta makaranta yasa naga ya dace na mika masa sakon gayyata.


‘’A cikin wannan watan za'ayi bikin ranar ilimi ta duniya, zan nemi alfarma a Kwankwasiyya Reporters TV, a bamu lokaci kyauta ko kuma na biya da kudina, yazo muyi wata gasa dashi, ya fado inganta ilimin da yake magana gwamnatin Ganduje tayi, nima na fado wanda gwamnatin Kwankwaso tayi.


‘’Zamu samu masana cigaban ilimi, wadanda ba 'yan siyasa ba, su zama alkalan gasa, za'a saka mana kai tsaye ne, yadda muna gabatarwa, alkalai na tantancewa a lokaci guda, muna kammalawa su sanar da sakamako nan take, amma cikin yaren nasara (English), za'ayi wannan fafatawa.


‘’Duk wanda aka cinye a hujjoji, zai koma bangaren wanda yayi nasara, ina fatan zai karbi wannan tayin." ― Inji shi


Matashin dai ya sanar da hakan ne, cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a wannan rana, wanda yake martani kan kalaman shugaban APC da yayi. 


A ganinku waye zai sha kaye cikinsu, mudai namu idanu


Post a Comment

4 Comments

  1. Ai ba sai an fada ba, shi sai dai yayi ikrarin ko da tsiya kawai.

    ReplyDelete
  2. Ai ba sai an fada ba, shi sai dai yayi ikrarin ko da tsiya kawai.

    ReplyDelete
  3. Ai ba sai an fada ba, shi sai dai yayi ikrarin ko da tsiya kawai.

    ReplyDelete
  4. Ai kowa yasan waye kwankwaso wlh kishinahi ga talakawa yasa ake batashi dukda bayada wani datti! Akwai wani Wawa Wai ko Ali baba ko waye? Waifa laifin kwankwaso akan wannan sakaran, idan talakawa Basu mantaba scholarship din kwankwaso. Yace" Banda yayan masu rike da mukaman gwamnati!!! Shine ya sako yayanshi! Jagora yace baiyardaba yayan talakawa kadai! Domin jagora yace baya Saba alkawali Kuma bazai yaudari talakawa ba. Shine wannan mutumin yaketa babatun banzan akan jagora kwankwaso! Ammandai talakawa masu hankali sunsan gaskiya Kuma sunsani dukkan mutanen dake yakar jagora kwankwaso, sunayine dan yaki aminta da kwasar dukiyar talakawa. Da yanke masu filaye dan abawa masu mukamin gwamnati. Abar talaka a banza dan bayada gata

    ReplyDelete