Wata Rana A Shekarar 2015, Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso Yayi Da Ya Jagorancin Bikin Karbar Sababbin Daliban Jami'ar Northwest Karo Na Uku, A Dakin Taro Na Coronation Dake Gidan Gwamantin Kano.
Jami'ar Northwest Dai Mallakin Jihar Kano Ce, Wacce Kwankwaso Ya Samar Da Ita, A Kaf Fadin Arewacin Najeriya Jihar Kano Ce Kawai Keda Jami'oi Guda Biyu Mallakin Jiha, Da Kwankwaso Ya Kirkiri, Guda Daya A Gwamantinsa Ta Farko, Guda Daya A Gwamantinsa Biyu, Wato Dai Duk Zangon Mulkinsa Saiya Gina Jami'a.
Lokacin Da Kwankwaso Ya Kuduri Aniyar Gina Jami'ar Farko Mallakin Kano A Shekarar 1999, Mutane Da Yawa Sunyi Tunanin Abin Bazai Yiwu Ba. Amma Kwankwaso Yayi Hakuri Don Nuna Kwarewarsa Akan Mafarkinsu. Gashi Abin Har Ya Zama Tarihi, Dalibai Sama Da 5000 Sun Kammala Karatu A Jami'ar Kimiyya Da Fasaha Dake Wudil (KUST University).
Bayan Shekaru Takwas Da Nuna Halin Ko In Kula Da Gwamantin Malam Ibrahim Shekarau Tayi Da Waccan Jami'a, Kwankwaso Yana Dawowa Zangon Mulkinsa Na Biyu, Ya Sake Ganowa Tare Da Farfado Da Jami'ar, Tun Daga Kan Dakin Karatu, Dakunan Koyon Tiyata, Dakunan Kwanan Dalibai, Duk Ya Gina A Jami'ar KUST.
An Fara Gudanar Da Jami'ar Northwest Wacce Kwankwaso Ya Gina A Zangon Mulkinsa Biyu A Wani Tsari Na Musamman Cikin Girmamawa. Ita Ce Jami'ar Farko A Najeriya Da Ta Fara Karatu Zangon Farko Da Dalibai 1,000, Tsangayu (Faculty) Guda 4, Sashen Karatu (Department) Guda 17, Shirye Shiryen Karatu (Program) Guda 24 Tare Da Malaman Jami'ar Guda 97 Da Suke Koyar Da Yanayin Ilimin Kimiyya, Tafiyar Da Ilimin Kimiyya Na Jama'a, Zane Zane Da Harsuna.
0 Comments