TAYA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA


Kungiyar Kwankwasiyya Reporters Nigeria, Karkashin Jagorancin Comr. Abdullahi Ghali Basaf, Na Mika Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranar Haihuwa Ga Mai Girma Jagoran Kwankwasiyya Na Karamar Hukumar Kumbotso Dake Jihar Kano, Kuma Jigo A Siyasar Nigeria Baki Daya, Dr.  Danyaro Ali Yakasai. 



Hakika Jagora Mutum Ne Mai Karamci Da Girmamawa, Dukkan Wani Kokarinsa Na Ganin Cigaban Kwankwasiyya A Bayyane Yake, Abinda Duk Kuma Yaga Zai Kawo Cikas, Yana Kokarin Maganceshi, Dukkan Nagartar Jagoranci Ta Tabbata A Gareshi, Musamman Adalci, Hakuri, Juriya Da Kuma Jajircewa. 


Muna Masa Fatan Alheri A Rayuwa, Allah Ya Kara Inganta Lafiya, Tsawon Rai Mai Amfani, Muna Kuma Addu'ar Allah Ya Kawo Babban Rabo Mai Amfani, Ya Bawa Kwankwasiyya Nasara A Dukkan Al'amura Da Suka Kasance Alheri. 



Post a Comment

0 Comments