Tattalin arziki: Ganduje yayi faduwar bakar tasa

 



Gwamnatin tarayya ta raba zummar kudi N123.348bn (USD324.6m), zuwa jihohi 32 da suka taka muhimmiyar rawa, amma jihar Kano ce ta karshe a rabauta da mafi karancin kudi na N1.710bn, kamar yadda ministan kudi, Zainab Shamsuna Ahmad, ta bayyana ta bakin daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar kudi, Hassan Dabo, a makon da ya gabata. 


Ministar tace, anyi wannan tsari ne bisa yanayin yadda jihohin suke gudanar da gwamnatinsu, musamman sanya kasafin kudi a yanar gizo, nuna gaskiya da yin kasafin kudin shekara a bude, tattala kudin al'umma, da kuma ragewa mutane radadi musamman rage musu haraji yayin cutar Covid19.


Jihar Sokoto dai itace tazo ta farko da zummar kudi N6.612bn, wanda hakan ke nuna gazawar gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, akan wadancan matakai na gwamnatin tarayya da ya gagara aikatawa, duk da dai wasu suna ganin a hakan ma yayi kokari, domin akwai jihohin da basu samu ko silai guda ba saboda gazawa, irinsu Bayelsa, Imo, River da kuma Zamfara.



Post a Comment

0 Comments