Prof. Sani Lawal: Bai Kamata Hukumar Zabe Ta Dinga Karbar Umarnin Yan Siyasa Ba

 



Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Malami Ne A Sashin Nazarin Halayya r Adam, A Jami'ar Bayero Dake Kano, Kuma Shine Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Jihar Kano (KANSIEC), Ya Bayyana Cewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kano, Wanda Za'a Gudanar Ranar Asabar Mai Zuwa, Zabe Ne Wanda Al'ummar Jihar Kano Ba Zasu Gamsu Da Ingancinsa, Saboda Rashin Aminci Da Ake Zargin Shugaban Hukumar Zaben, Da Kuma Gwamnatin Jihar Kano. 


Cikin Zantawarsa A Daya Daga Cikin Gidajen Redeyoyin Kano, A Wannabe Makon Da Muke Ciki, Farfesa Malumfashi, Yace Tun Farko Gazawar Hukumar Ne Yasa Jam'iyyun Adawa Suka Kauracewa Shiga Zaben, Domin Kamata Yayi Hukumar Ta Kafa Kwamiti Na Musamman, Wanda Mambobinsa Zasu Kunshi Wakilcin Kowacce Jam'iyya, Hakan Shine Zaisa Jam'iyyun Su Gamsu Hukumar Na Tare Dasu, Ba Kawai Hukumar Ta Dinga Mu'amala Da Jam'iyya Guda Daya Ba.


Farfesa Malumfashi, Yace A Yanzu Dai Wannan Hukuma Ba Zaman Kanta Take Ba, Amma A Lokacinsa Ne Yayi Abinda Ya Dace, Domin Shine Shugaban Da Yayi Watsi Da Umarnin Gwamna, A Lokacin Da Aka Bashi Umarnin Daga Zabe, Sakamakon Rahoton Barazanar Tsaro Da Gwamnati Ta Samu, Shi Yasa A Yanzu Ya Bawa Shugaban Hukumar Zabe Ta Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka, Shawarar Ya Kauracewa Karbar Umarnin Yan Siyasa, Domin Hukumar Zaman Kanta Take. 


"Ranar Juma'a Aka Aikomin Na Daga Zabe, Sai Na Tashi Na Tafi Gidan Gwamnati, Na Samu Gwamna Kwankwaso Nace Ranka Ya Dade Me Yasa Kace A Daga Zabe? Sai Yace Mun Samu Barazanar Rashin Tsaro Ne, Sai Nace Masa Babu Abinda Zai Faru Ranka Ya Dade, Gobe Asabar Ne Wannan Zaben, Barazanar Da Zamu Samu Idan Muka Daga Tafi Wacce Zamu Samu Yanzu, Kuma Ina Tabbatar Maka, Kaso 90% Na Mutane Suna Tare Dakai, Domin Nayi Bincike Na Gano.


"Bayan Anyi Zabe, Jam'iyyar Kwankwaso Ta Cinye Dukkan Kujerun Ciyamomi Da Kansiloli, Wannan Ya Tabbatarwa Da Gwamna Cewa Tabbas Bincikena Ba Jabu Bane, Haka Kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa INEC, Itama Sakamakonta Na Babban Zaben 2015 Ya Nuna Cewa Jam'iyyar Kwankwaso Ce Ta Cinye Zaben Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa, Sanatoci Guda Uku, Yan Majalisar Tarayya Guda 24, Yan Majalisar Jiha Guda 40, Ko Kujera Daya Jam'iyyun Adawa Basu Samu Ba.


"Dole Nayi Alfahari Kan Sahihin Zaben Kananan Hukumomi Dana Gudanar A Jihar Kano, Ban Bari Wani Ya Shigar Min Aikina Ba, Kuma Tun Ana Saura Kwana Uku Zabe, Nake Umartar Dukkan Ma'aikatan Hukumar, Kowa Ya Debo Kayansa Da Abin Goge Baki, Anan Muke Kwana Har Sai An Kammala Zabe An Bayyana Sakamako, Ina Bawa Na Yanzu Shawara, Su Dauki Salon Adalci Da Mukayi Amfani Dashi Domin Samun Nasara, Ta Yadda Za'ayi Alfahari Dasu Ko Bayan Basa Nan." ~ Farfesa Sani Lawal 


Post a Comment

0 Comments