Masarautar Argungun Ta Karrama Kwankwasiyya Da Sarauta

 Masarautar Argungun Ta Karrama Kwankwasiyya  Da Sarauta 





Mai Martaba Sarkin Argungun, Alhaji Sama'ila Muhammad Mera, Ya Nada Jagoran Kwankwasiyya Na Jihohin Kebbi, Sokoto Da Zamfara, Injiniya Abubakar Sadiq Argungun, A Matsayin "Jakadan Kabi" Sarauta Irinta Ta Farko A Wannan Masarauta, Wacce Take Bada Damar Magana Da Yawun Sarki, Ko Kuma Wakiltarsa A Wajen Wani Taro Da Bazai Samu Halarta Ba. 


A Ranar Asabar Din Da Ta Gabata 02/01/2021 Ne, Akayi Bikin Nadin Masarautar, A Fadar Masarautar Argungun, Wanda Manya Manyan Mutane Daga Sassa Daban Daban Na Nigeria Suka Halarta, Kama Daga Kan Sarakai, Malamai, Yan Siyasa Da Sauran Al'umma, Kamar Yadda Sakataren Yada Labaran Kwankwasiyya Na Jihar Kebbi, Barr. Bala Bawa Baraje, Ya Bayyanawa Wakilinmu Abubakar Lecturer. 


Mahalarta Taron Sun Hada Da, Dan Majalisar Dokokin Jiha Na Karamar Hukumar Suru, Alhaji Umar Danfari Suru, Shugaban Kwankwasiyya Na Kebbi Hon. Isah Yakubu Fakai, Shugabannin Kwankwasiyya Na Sokoto Da Zamfara, Shugaban Dattawan Kwankwasiyya Na Jihar Kebbi, Alhaji Musa Uba Dawaki Yauri, Alhaji Nura Hussaini President, Alhaji Yusuf Kamba, Alhaji Muhammad Yauri. 


Fitaccen Mawakin Kwankwasiyya, Tijjani Gandu, Tare Da Jama'arsa Sun Samu Halarta Wannan Bikin Nadin Sarauta Na "Jakadan Kabi" Wanda Aka Yiwa Engr. Abubakar Sadiq Argungun, Sarauta Irinta Ta Farko A Tarihin Masarauta.



Post a Comment

0 Comments