Tabbas:- BA RABO DA GWANI BA
Wannan Karin Magana ta ba haushe na fara tunawa jiya lokacin da naji wani babba a gidan freedom cikin shirinsu na kowanne gauta yana magana kamar da Aradu akan irin kisan mummuken da akewa kano da kanawa a wannan gwamnatin ta Buhari, Naji yadda ya kawo illar da Filin tashi da saukar jirage na kasa da kasa na malam Aminu Kano ke fuskanta duba da cewa ita dai kanon ita akewa laƙabi da cibiyar kasuwanci a wannan kasa tamu Nigeri.
Wannan ce ta tuna min tsohon dan Majalissar Tarayya na Dala kuma dan takarar sanatan Kano ta tsakiya Hon. Aliyu Sani Madakin Gini, Na kuma tuna da irin gwagwarmayar da yayi a majalissa lokacin harma rikici sosai da gwamnatin tarayya hade da ministar Harkokin Jiragen Sama a wancan lokacin wato MRS. STELLA OGIEMWONYI ODUAH Duba da yadda ta nemi kashe filin jirgin na Aminu Kano Har Sai da ta kai ta kawo jiragen da suka taso daga wata kasar ba zasu sauka a Kano ba, sai da su sauka a lagos ko Abuja ko Enugu ko da kuma Kanon zasu zo, Sai dai bayan sun sauka acan sannan su sake hawa wani jirgin mai jigila a cikin gida sannan suzo kano, a karshe sai ma muka jiwo gwamnatin tarayya a wannan lokacin ta fitar da sanarwar zata chefanar da filin jirgin Malam Aminu Kano dake cikin birnin na kanon dabo.
Hakika Aliyu Sani Madaki Yayi kokari a wancan lokacin kasancewarsa Dan Jihar Kano mai kishin jihar kano dole ne ya tsaya tsayin daka wajen kare martabar jihar kano da kimarta ta idon duniya, shi kadai ne muka jin muryoyinsa a majalissar idan yana magana saboda kamar Ransa Zai fita saboda bakin cikin abinda ke faruwa, Amma cikin Yaddar Allah da huwacewar Har sai da Aliyu Madaki yayi nasara akan daƙile duk wata mummunar manufa da aka ƙulla yiwa Filin Jirgin Malam Aminu Kano, sannan ya Madaki ya samu Nutsuwa.
Amma Kuma Yanzu Sai Muka Sake Jiwo Wata ƙullalliyar a gwamnatin Dan Arewa Kuma Wadda Yake tutiyar cewa Kano ita ce Cibiyar Siyasarsa.
0 Comments