Shakka babu yanzu gabadaya yan siyasar Nigeria masu juya akalar mulki babu wanda yaja matasa maza da mata a jikinshi wajen ginasu tare da yi musu jagoranci wajen yadda zasu zama mutanen kansu tare da jajircewa wajen nemawa kasarsu ta Nigeria yanayi mai kyau ta fuskar democradiyya sama da Sen (Dr) Rabi'u Musa Kwankwaso.
Na tabbata mai karutu zai yarda dani, idan nace yanzu kaf fadin Arewacin kasar Nigeria babu wani dan siyasa da alumma suke kallo a matsayin jagora sama da kwankwaso duba da yarda ya tafiyar da mulkinshi a baya a jihar da tafi kowacce jiha girma da yawan alumma a Arewacin Nigeria (KANO). Azamanin da yake mulkinshi, sanin kowa ne yadda Mai Girma kwankwason ya dunga fito da tsaruka masu inganci wajen ciyar da jihar gaba ta fanninka more rayuwa musamman wajen nemawa maza da mata sana'oin dogaro da kai da sauransu.
Mafi kyautuwa ga alumma irin tamu ta Arewa shine bawa matasa ilimi mussamman duba da matsolilin da suka addabe mu, kama daga , tabarbarewar tsaro, ilimi, lafiya da sauransu.
Kwankwaso ya zamanto zakaran gwajin dafi wajen kawo tsaruka masu inganci wayanda idan akabi su zasu zama taswira wajen fidda kasar nigeria daga cikin halin rashin tsaro da zaman lafiya da ya addabe mu. maida hankali kan bawa matasa maza da mata ilimi kyauta domin dogoro da kansu tare da kawo saukin zaman banza yana daya daga cikin manyan dirkoki da ya kamata ayi amfani dasu wajen kawo karshen matsalar tsaro da zaman lafiya a cikin alumma irin tamu. Wannan yana daya daga cikin tsarin Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso dan kuwa duniya ta shaida cewa yanayi ana gani.
Baya ga wannan, Kwankwaso ya kafa tarihi akan jihar kano na fito da ingantattun tsaruka na ciyar da alumma gaba wayanda wasu daga cikin jihohin Arewa suke kokarin kwafa a koda yaushe domin samarwa alummarsu mafita mai kyau. Kwankwaso shine gwamna na farko a Arewacin Nigeria da ya fara Aurar da zawarawa , shine ya fara manyan gine gine masu fito da darajar kasa domin ci gaban jiha, shine ya fara bawa yara ilimi kyauta, shine ya fara samar da hukumomi masu saita al'amuran alumma na yau da kullum domin samar da zaman lafiya irinsu HISBAH, KAROTA da Sauransu. haka zalika shine gwamna na farko a Nigeria da yataba assasa manyan Jami'oi har guda biyu tare da gina polytechnics da dama a jihar sa domin inganta harkar ilimi.
Dan haka nake ganin ko iya nan na tsaya a irin abubuwan ci gaba da Mai Girma Jagora Rab'iu kwankwaso ya samarwa alummarsa, a matsayina na dan gwagwarmaya yakamata ace bani da wata alkibla ta siyasa sama dashi. Dan kuwa duk wanda yace yana gwargwarmaya ne domin samarwa kansa da alummar sa mafita mai inganci, babu abinda ya kamata yayi illa kallo ga shuwagabanni na gaba, ya duba yaga wanda ya tabbatar da gaske yakeyi , (yayi an gani ba zato ba, yayi abubuwan da ido zai gani, hannu zai taba , kafa zata taka, baki zai fada) ya goya mashi baya domin samun tabarraki tare da jajircewa wajen kara karatun yarda yakamata yatafiyar da kanka a duk lokacin da Allah yasa ya tsinci kanshi a harka ta shugabanci kowanne iri ne a rayuwa.
Na tabbata a nawa lissafin da mafi yawancin lissafin mutane da nakeji, babu wani shugaba daga arewa mussaman wanda ya rike kujerar gwamna kuma yake neman shugabancin kasa a yanzu da idan ka daura shi akan maunin sikeli na wayannan abubuwa da na lissafo na ci gaba zai rinjayi Dr Rabiu Musa Kwankwaso. Dan haka na yarda cewa duk wani matashi dan gwagwarmaya mai yi da daske dan Allah , dan samun ci gaban kanshi da alummar shi, bashi da wata alkibla ta siyasa democradiyya da ya cancanta ya kalla sama da Kwankwaso.
Wannan ra'ayina ne a matsayina na dan gwagwarmaya mai son ci gabanshi da ci gaban alummar kasarshi. Da wannan nake yiwa Jagora Fata Allah ubangiji ya zaba mashi mafi alkhairi 2023. Allah ya bashi shugabancin Kasar Nigeria kuma ya rike mashi yayi mashi jagora wajen kawowa alumma mafita mai inganci.
0 Comments