Siyasar Kwankwasiyya A Nigeria, Karkashin Jagorancin Jagora Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, Tasha Alwashin Kawo Karshen Shaye Shaye Musamman A Jihar Kano, Duba Da Yadda Hannun Agogo Ya Dawo Baya Akan Harkar Shaye Shaye, Idan Akayi La'akari Da Yadda Gwamnatin Kwankwasiyya Ta Kakkabe Shaye Shaye A Fadin Jihar Kano, Musamman Wajen Samar Da Makarantar Gyaran Tarbiyya (Kano Reformatory Institute) A Karamar Hukumar Kiru, Cikin Jihar Kano.
Hakan Ya Fito Ne Daga Bakin Mai Magana Da Yawun Kwankwasiyya Na Kasa, Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, Yayin Da Kungiyar Nan Mai Rajin Yaki Da Shaye Shaye (Youth Movement Against Drug Abuse), Take Karrama Dan Takarar Gwamnan Kano Na Jam'iyyar PDP A Zaben 2019, Engr. Abba Kabir Yusuf, A Makon Da Ya Gabata, Bisa Kokarinsa Na Yaki Da Shaye Shaye Da Keta Haddin Mata A Jihar Kano Da Nigeria Baki, Musamman Lokacin Da Yake Kwamishinan Ayyuka, Sufuri Da Gidaje A Gwamnatin Kwankwasiyya A Jihar Kano.
Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, Wanda Ya Karbi Shaidar Karramar A Madadin Abba, Yayi Godiya Ga Wannan Kungiya Tare Da Tabbatar Musu Cewa Zasu Cigaba Da Kokari Akan Gyaran Tarbiyyar Matasa, Domin Yanzu Haka Ma Jagoran Kwankwasiyya, Yana Tsaka Da Kokarin Samar Da Makarantar Gyaran Tarbiyya Mai Zaman Kanta, Tunda Dai Gwamnatin Ganduje Ta Rufe Wacce Suka A Gwamnati.
1 Comments
That is a very good I'm waiting for you
ReplyDelete