An sace wayoyin yan jarida a zaben kananan hukumomin Kano

  



Wakilin jaridar Daily Trust, wanda ya gudanar da aikinsa a Tudun Bojuwa, rumfar zabe ta Kurna, a yankin karamar hukumar Dala ta jihar Kano, ya hadu da wasu yan jagaliyan siyasa, wadanda suka karbe masa wayarsa, sannan suka goge dukkan hotuna da bidiyoyin da ya dauka a rumfar zaben. 


Daily Trust, ta rawaito cewa, wakilin nasu ya fuskanci barazana da rayuwarsa daga yan daban, suka kwace masa wayar tasa bisa zargin yana daukarsu a bidiyo, sannan daga bisani suka kirawo iyayen gidansu na siyasa tare da bukatar yan sanda su kama wakilin nasu. 


Bayan ankai ruwa rana, sun bashi wayar tasa, amma sun goge dukkan hotuna da bidiyoyin kan wayar, wacce da ita yake hada rahotonsa, yana tsakar aikinsa yan daban suka zo masa, da zargin dan leken asirin siyasar Kwankwasiyya ne, wacce take adawa da bangaren masu mulki.


A makamancin wannan, cikin makarantar yan mata ta larabci dake karamar hukumar Bichi, wani jami'in jam'iyyar APC, yayi barazana ga wani dan rahoton jaridar Daily Trust, yace masa yabar wajen ko kuma suyi masa rashin mutunci. 


A wannan rana ne dai aka gudanar da zaben kananan hukumomi na ciyamomi da kansiloli a fadin jihar Kano, karkashin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC). 


Post a Comment

0 Comments