Alh Zubairu Katirje :Yanzu Mutane Kowa Yaji Ajikinsa

 



A lokacin mulkin Buhari na farko ya takurawa masu kudi da sarakuna, kasan shi talaka  yanaso yaga antakurawa wanda ya fishi wani abu, shiyasa a lokacin da yawa talakawa suke sonsa.              Kuma wani abu da mutane basu sani ba shine, Kayan abinci da Gwamnati Buhari take rabawa a wannan lokaci bashine ya siyosu ba. 


Gwamnatin Shagari itace tayo odarsu daga waje kafin suzo a fara rabawa Buhari yayi masa juyin mulki, shine kayan sukazo a lokacin da Buhari ya karbi mulki.


 Kuma a lokaci ya chanja kudin kasar baki daya a dan takaitacen lokaci wanda bai wuce sati biyu ba, a wannan lokacin mutum da kudinsa amma yanaji yana gani zaiyi asararsu kokuma a sayar masa da kaya ya bada kudin, kuma kudin ankarya darajar su, domin idan aka baka kayan  naira biyar sai kabada naira takwas a tsohon kudi, kaga gaba akaci ko baya.   


 Haka gwamnatinnan tazo tabi 'yan kasuwa tayi ta karyasu, za kaje ka siyo kaya da tsada gwamnatin tazo ta karya kayanka tasiyar, kai a lokacin har wasu manyan mutane gwamnatin ta daure irin su Khalifa Isyaka Rabi'u da sauran mutane da yawa.   


Haka aka zo idan kadubi  daga lokacin da ya karbi wannan mulkin a 2015 yace duk wa 'yanda sukayi abaya basu iyaba, amma kafin yacika shekara guda mutane suka kasa gane inda gwamnati ta dosa.   


 Yau da muke maganarnan dakai saura 'yan kwanaki kadan a cika shekara biyu da zaben Shugaban kasa karo nabiyu amma har yanzu babu wani chanji mai anfani, kuma haka gwamnati zata kare babu wani  abu da zata iya saboda idan kaduba zuwa karshen shekarar  nan da za'a shiga cikin siyasa ake dumu-dumu, Kaga ana guguwar siyasa aiki bazai yuwu ba, to da yaushe za'ayi aikin, Shiyasa nace mutane jiki magayi, yanzu kowa yaji a jikinsa.


Wannan itace takai tacciyar Hirata da Alh Zubairu Katirje UN/TUDU Ward Daya daga cikin Jagorori na PDP Kwankwasiyya a Karamar Hukumar Gwarzo



Post a Comment

0 Comments