Banyi tsammanin sadaukarwa da jajircewar Zakakuran sojojin Najeriya da suka mutu zai kasance aikin baban giwa ba, a iyakar tunani na waɗannan mutane da suka hadu da wanga ibtila'i zasu samu mutuntawa da kuma darajawa sakamakon sadaukarwar su gare mu baki daya.
Babu jiha daya tilo a Najeriya wanda sojoji basa aikin wanzar da zaman lafiya, duk da cewar ba aikin su bane. Duk jihar da kaje a halin yanzu sai ka samu sojoji suna fadi tashin ganin zaman lafiya ya wanzu.
Amma duk da irin wannan hubbasa da soja keyi, sai gashi gwamnoni musamman na Arewacin ƙasarnan wadanda tsaro ya tabarbare a jihohin su suna sharholiyar bikin aure, sun gaza halartar Jana'izar shugaban sojojin dake aikin wanzar da zaman lafiya a jihohin su.
Nayi tsammanin ganin cincirindon gwamnonin Arewa a wajen Jana'izar zaratan sojojin mu, amma kash! Suna Kano suna gasa yatsu a wajen biki.
0 Comments