Ko mutum baije Kaduna ba, yana da damar sanin yadda zata kasance!

 



Tuni wasu daga cikin wakilanmu na sashen gidan talabijin na Kwankwasiyya Reporters suka isa jihar Kaduna, yayin da wasu ke kan hanyarsu ta zuwa, domin kawo rahotanni kai tsaye, bisa yadda zata kasance a wajen taron zaben shugabannin jam'iyyar PDP reshen Arewa maso yamma, da za'a gudanar a kasuwar Trade fair dake Kaduna. 


Ku kasance da shafukanmu na facebook, Kwankwasiyya Reporters, da Kwankwasiyya Reporters TV, da sauran shafukanmu na facebook, twitter, instagram da sauransu, tun daga misalin karfe 10:00am na safe a wannan rana, domin ganin yadda taron zai kasance, musamman ga wadanda basu samu damar halarta ba, zaku kalla tamkar kuna wajen. 


Ubangiji Allah yasa ayi taro lafiya a tashi lafiya, dukkan wani abin ki Allah ya tsare, yasa kowa yaje lafiya ya dawo lafiya. Ameen. 


Mungode 


Post a Comment

0 Comments