Zanyi Matukar Mamaki Idan Naga Dan Arewa Musamman Dan Jihar Kano In Ganshi Yana Tallar Tsohon Gwamnan Jihar Lagos Wato Bola Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya.
Da Farko Dai Kafin In Yi Magana Ta Kai Tsaye Ya Kamata Mu Jajantawa Tare Da Yin Danniyar Kirjin Al'ummar Jihar Kano Bisa Zuwan Shi Tinubu Zuwa Jihar Kano Domin Yin Bikin Cika Shekarunsa Da Bamu San Takamaiman Nawa Bane, A Wannan Bikin Birthday An Kashe Makudan Kudade A Wannan Jiha Tamu Amma Har Yanzu Ba'a Biya Ma'aikatan Gwamnati Albashinsu Ba.
Da Farko Shin Wanene Tinubu A Kano?
Menene Bola Tinubu A Wajen Kanawa?
Wacce Irin Gudunmawa Ya Bawa Kanawa?
Shin Tallafi Ya Bawa Alummar Jihar Kano?
Akwai Lokacin Da Aka Dunga Kona Gidajen Y'an Kano A Jihar Lagos Wacce Irin Gudunmawa Bola Tinubu Ya Bayar?
Ya Kamata Ace Mai Kishin Ka Kana Kishin Sa,
Bola Tinubu Shine Shugaban Siyasar Jihar Legas, Yayi Gwamnan Jihar Legas Hawa Biyu Kuma Shine Jagoran Siyasa Kusan Yanzu Na Yammacin Najeriya, Yana Ma Dukan Kirjin Cewa Shine Jagoran Jam'iyyar APC Na Kasa Baki Daya Amma Aka Kamo Y'an Uwanmu Masu Hayar Babura A Legas Ana Kullewa, Aka Kama Mutane 180 Aka Kulle Babu Dalili, Aka Rufesu A Gidan Kurkuku Ba Tare Da An Fada Musu Laifinsu Ba Kuma Ba Tare Da An Kaisu Kotu Ba Har Sai Da Jagoran Kwankwasiyya Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Samu Labari Ya Tashi Ya Tafi Legas, Kuma Maimakon Suji Kunya Su Bada Hakuri Su Bashi Mutanen Nan Duka, Amma Sai Suka Yi Tabarmar Kunya Suka Taso Da Rikici Da Hayaniya Wanda Har A Lokacin Gidan Jaridar Tinubu 'TTHE NATION' Tace Yana Nuna Kabilanci Don Me Zai Zo, Daga Karshe Dai Suka
Gama Hayaniyar Sai Aka Tafi Kotu Aka Zabga Makudan Kudade Aka Ce Sai An Biya Kudin Belinsu, Da Aka Kawo Takardu Aka Sa Hannu, A Cikin Mutanen Da Aka Kama Akwai Y'an Jihar Kano Akwai Na Zamfara Akwai Na Sokoto Akwai Na Kebbi Da Sauran Wasu Daga Cikin Yan Arewa, Aka Karbo Belin Mutanen Nan Amma Ina Jin Mutum Hudu Ko Zuwa Shids Sun Mutu A Kurkukun Nan, Amma Bola Tinubu Kalma Daya Baiyi Ba Akan Abinda Ya Faru Ga Y'an Arewa A Jiharsa, Baice Gwamnatin Legas Bata Kyauta Ba, Bai Shiga Maganar Ba Lokacin Da Aka Je Belinsu, Bai Ce Ga Gudunmawarsa Ba Bayan Sun Fito Daga Kurkukun Ba Bai Yi Musu Jaje Ba.
A Abeokuta Ma Haka Aka Yi, A Shekarar 2018 Wata Y'ar Matsala Ta Taso Aka Rinka Bin Gida Ana Kona Gidajen Mutanenmu Na Arewa, A Lokacin Engr Rabiu Kwankwaso Ya Zabura Ya Kai Gwauro Ya Kai Mari, Aka Tuntubi Gwamnan Jihar To Da Yake Shi Gwamnan Ma Yana Da Kirki Sai Da Ya Tsaya Tsayin Daka Sai Da Aka Kashe Maganar, Yasa Dokar Ta 6aci Sannan Yayi Ta Tuntubar Kwankwaso Wanda Har Ta Kai Ga Sai Da Keankwaso Ya Kai Musu Gudunmawa Ya Basu Shawarwari Sannan Ya Zauna Dasu Tare Da Karfafa Musu Gwiwa, A Nan Ma Bamu Ji Magana Ko Daya Wadda Bola Tinubu Yayi Ba, Ba Muji Inda Ya Taimaki Wadannan Bayin Allah Da Suka Rasa Dukiyoyinsu Ba.
A Kwanan Nan Anyi Rikici A Ibadan Dake Jihar Oyo Inda Aka Konawa Hausawanmu Shagunan Sana'o'insu Da Kuma Su Kansu Aka Rinka Kashe Su Ana Kona Wasu Amma Har Yanzu Kalma Daya Bai Fada Ba Akan Abinda Ya Faru Ba Daidai Bane, Bai Ce A Matsayina Tsohon Gwamnan Jihar Legas, A Matsayina Na Jagoran Siyasa Na Kasar Yarabawa, A Matsayina Na Tsohon Sanata, A Matsayina Na Mai Kwadayin Takarar Sugabancin Kasar Najeriya Kuma Ga Gudunmawa Kuma Y'an Najeriya Ne Abinda Akayi Muku Ba'a Kyauta Ba An Cuce Ku, Ko Kadan Bai Yi Hakan Ba.
Daga Karshen Takaitawa Don Allah Mai Karatu Ina So A Fada Min Wanene Bola Tinubu Musamman A Jihar Kano? Wanene Bola Tinubu A Wajen Y'an Arewa Musamman Kanawa?
Me Yayiwa Kano Da Kanawa?
Wanne Irin Kallo Yake Mana Kuma Muna Wanne Irin Kallo Ya Kamata Muyi Masa?
A Wanne Dalilin Za'a Daukoshi A Kawoshi Gidan Gwamnatin Kano A Dauko Makudan Kudade A Narka Domin A Tayashi Murnar Cika Shekarun Da Bamu San Adadinsu Ba?
Na Takaita A Nan.
0 Comments